Miji ya wurgo matarsa daga saman bene saboda ta cika yawo

Miji ya wurgo matarsa daga saman bene saboda ta cika yawo

Wani abin takaici ya faru a garin Ikko, cunkus dakin tsumma, wato jihar Legas inda wani mutum ya jefo matarsa daga saman bene saboda a cewarsa ta cika yawo kamar kaza.

Miji ya wurgo matarsa daga saman bene saboda ta cika yawo

A ranar Alhamis 29 ga watan Disamba ne aka gurfanar da mijin matar Kema Akejelu mai shekaru 33 gaban kotun majistri na Ikeja inda ake zarginsa da laifin bugun matarsa da jefo ta daga saman bene.

KU KARANTA:Yan mata biyu sunyi doke doke akan Saurayi

Inspekta Simeon Inuoha wanda shine dansandan daya shigar da kara yace “wanda ake zargin ya cillo matarsa ne daga gidan bene hawa daya, wanda hakan yayi sanadiyyar targadewar gwiwowin hannayenta biyu.”

Sai dai wanda ake kara ya musanta zargin da aka yi masa, daga bisani kuma kotu ta bada belinsa akan kudi N50,000 da wani tsayayye guda daya, sa’annan kotu ta daga sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Feburairu na shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel