Gwamnan Jigawa ya kori shugabannin riko 3

Gwamnan Jigawa ya kori shugabannin riko 3

- Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya sallami wasu shuwagabannin riko na kananan hokumomi uku a jihar

- Ba’ a bayara da daliln korarsu ba sai dai ana zargin cewa hakan na da nasaba da rikicin kasafin kudi ba

Gwamnan Jigawa ya kori shugabannin riko 3
Gwamnan Jigawa ya kori shugabannin riko 3

Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya sallami wasu shuwagabannin riko na kananan hokumomi uku a jihar

An bayyana korari ne a wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini ya sa hannu.

Sanarwar ta ce, kananan hukumomin su ne Guri, da Jahun, da kuma Birniwa, sannan sanarwar ta kuma umarci shuwagabannin da a ka sallama da su mika ragamar kananan hukomomin ga daraktocin gudanarwa kamar yadda The Nation ta rawaito.

Gwamnatin ta kuma godewa shuwagabannin bisa bautawa jihar da su ka yi, ta kuma yi ma su fatan alheri yayin da su ke komawa kan ayyukansu.

Duk da cewa ba a bayyana laifin da tsaffin shuwagabannin su ka yi ba, ba zai rasa nasaba da rikicin Kasafin kudi a kananan hukmomin nasu ba.

A ranar Laraba ne 28 da ga watan Disamba, gwamnan jihar Jigawa ya yi taro da wasu shuwagabannin kananan hukmomi har zuwa tsakar dare a inda ya bayar da umarnin cire shuwagabannin kananan hukmomi uku.

A watan Agusta ma dai gwamnan ya sallami kwamishinan kasa da gidaje da kuma ci gaban alkarya, Adamu Sarki.

Sakataren gwamnatin jihar ya kuma ce, gwamna Badaru ka iya sallamar duk wani mai rike da mukamin siyasa matsawar a ka daina jin dadin aikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel