Babban ma’aikacin gwamnati yayi gaba da motoci 40

Babban ma’aikacin gwamnati yayi gaba da motoci 40

– Gwamnatin Shugaba Buhari na bi a hankali wajen yaki da rashawa a Kasar

– Ministan watsa labarai na kasar ya bayyana haka

– Alhaji Lai Muhammad yace wasu suna kokarin nuna ba haka lamarin yake ba

Babban Ma’aikacin Gwamnati yayi gaba da motoci 40
Babban Ma’aikacin Gwamnati yayi gaba da motoci 40

Ministan watsa labarai da al’adu na Kasar nan, Alhaji Lai Muhammad, ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari na bi a hankali wajen fada da cin hanci da rashawa a Najeriya. Ministan ne dai ya bayyana haka da kan sa a Yau da yake Legas.

Hakan na zuwa ne bayan da Ministan ya bayyana cewa an kama wani Babban Jami’in Gwamnati da yayi awon gaba da manyan motoci kirar SUV har guda 40. Wani Sakataren din-din-din ya kasa-ya rabawa kan sa wadannan motoci shi kadai ba tare da ko Bismillah ba.

KU KARANTA: Yan Matan Chibok: Gwamna yayi jawabi

Lai Muhammad ya bayyana irin matakan da Gwamnatin Kasar ta ke bi domin hana cin hanci da rashawa. Lai Muhammad yace an kawo tsarin nan na asusun bai daya watau TSA, sannan kuma an nada Kwamiti da dama domin su tattara abin da Gwamnati ta karbo daga hannun barayin Kasar.

Kwanan nan ne ma dai gwamnatin ta kawo wani tsari na tona asiri-ka-samu-kason ka. Sannan kuma an gano ma’aikatan bogi da dama wanda albashin sun a shekara ya kai Naira Biliyan 200.

Asali: Legit.ng

Online view pixel