‘Yan Boko Haram na garkuwa da 'Yan matan Chibok

‘Yan Boko Haram na garkuwa da 'Yan matan Chibok

- Rundunar sojin Najeriya ta ce, mai yiwuwa be 'yan Boko Haram su yi garkuwa da wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka kama yayin da su ke tserewa daga dajin Sambisa

- A ranar Juma'a 24 ga watan Disamba ne sojojin su ka kama sansanin ‘yan Boko Haram na karshe da suka yi wa lakabi da ‘Camp Zero’ wanda kuma shi ne babbar matattarar 'yan ta'addan ne

‘Yan Boko Haram na garkuwa da 'Yan matan Chibok
Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da tare da Mataimakin Shugaban Kasa a yayin bikin cetosu

Rundunar sojin Najeriya ta ce, mai yiwuwa be 'yan Boko Haram su yi garkuwa da wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka kama yayin da su ke tserewa daga dajin Sambisa.

A ranar Juma'a 24 ga watan Disamba ne sojojin su ka kama sansanin ‘yan Boko Haram na karshe da suka yi wa lakabi da ‘Camp Zero’ wanda kuma shi ne babbar matattarar 'yan ta'addan.

Kuma an rawaito cewa, wasu mayakan na Boko Haram sun tsere. Yayin da ba a samu 'yan matan Chibok ko daya ba a yayin farmakin sojojin.

An kuma rawaito cewa, ta yiwu 'yan ta'addan sun tafi da su, kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito cewa, kwamandan yakin 'Lafiya Dole' Lucky Irabor ya ce, ta yiwu 'yan ta'addan sun yi garkuwa da wasu daga cikin 'yan matan yayin da su ke tserewa daga dajin Sambisa wanda shi ne dalilin da ya sa ba a far musu ta sama ba. Ya ce:

"Gajiyayyun mayakan sun yi amfani da su ('yan matan) ne a matsayin garkuwa. Shi ne ya sa ba mu afka ma su ta sama ba."

A farkon makon nan ne rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kwato sansanin 'yan Boko Haram na karshe a dajin Sambisa, tare da fatattkar 'yan ta'addan, amma babu labarin sauran 'yan matan na Chibok da ke hannunsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel