Sunday Oliseh ya samu kungiyar horarwa a kasar Holland

Sunday Oliseh ya samu kungiyar horarwa a kasar Holland

An nada tsohon dan wasan Super Eagles kuma jagoran dan wasan kungiyar Sunday Oliseh a matsayin mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Fortuna Sittard dake kwallo a rukuni na biyu na gasar cin kofin kasar Holland a nahiyar Turai.

Sunday Oliseh ya samu kungiyar horarwa a kasar Holland
Sunday Oliseh ya samu kungiyar horarwa a kasar Holland

Kungiyar Fortuna Sittard ne suka bayyana haka a shafin yanar gizonta inda tace Oliseh ya rattafa hannu kan kwantaragin watanni 18, amma yana da damar kara tsawon kwantaragin nasa. Ana sa ran Oliseh zai fara aikin a ranar 2 ga watan Janairu na 2017.

KU KARANTA:Da kudin Oscar, zamu siyo wadannan yan wasan (Karanta)

Shima mai kungiyar Fortuna Sittard, Isitan Gün ya bayyana farin cikinsa, yayin dayake sanar da hayan Oliseh, a cewarsa sun yiyo hayar Oliseh ne saboda tarin kwarewa dayake da shi, sa’annan yan wasan kungiyar zasu dauke shi abin koyi.

Idan za’a iya tunawa Oliseh mai shekaru 42 yayi murabus daga kungiyar Super Eagles a watan Feburairu na shekarar 2016 bayan kwashe watanni 10 yana horar da kungiyar, sakamakon rashin samun goyon baya daga hukumar kwallon kafa ta kasa.

Sa’annan Oliseh ya buga ma Super Eagles ya buga wasanni 63, kuma ya buga ma kungiyoyi da dama da suka hada da Juventus da Borussia Dortmund. Bugu da kari, a baya ma Oliseh ya taba horar da kungiyar Vervietois kafin ya dawo Najeriya.

Za'a cigaba da samun labaran mu a nan ko a nan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel