Dan sanda, ma’aikacin banki sun hada baki wajen fashi a jihar Ribas

Dan sanda, ma’aikacin banki sun hada baki wajen fashi a jihar Ribas

- Jami’an yan sanda sun damke Sergeant Ukwuoma da wani ma’aikacin bankin Access Bank,Samuel Ndudiri, akan zargin hada baki da wasu yan baranda

- Ndudiri ne ya shirya fashi da makamin a bankin Access Bank inda asirinsu ya tonu

- Yan sanda sunce suna iyakan kokarinsu wajen kama sauran yan barandan da suka guje

Dan sanda,ma’aikacin banki sun hada baki wajen fashi a jihar Ribas
Dan sanda,ma’aikacin banki sun hada baki wajen fashi a jihar Ribas

Ofishin yan sandan jihar Ribas ta tabattar da rahoton damke wani Sajan Promise Ukwouma da ma’aikacin banki Samuel Ndudiri ,da laifin hada baki waje shirya fashi a bankin Access.

Game da rahoton jaridar Punch, an damke su biyun ne a ranan juma’a ,23 ga wtaan Disamba,bayan gudanar da wani binciken da jami’an liken asirin yan sanda suka yi.

Zaku tuna cewa jami’an sun kawo agaji banki inda wasu yan fashi suka kai hari bankin a ranan Alhamis,22 ga watan Disamba kuma suka damke mutane 3. 

KU KARANTA: Dajin Sambisa zai zama sansanin horo

Yan fashin sun shiga bankin ne da gwangwanin iskar gas a Access Bank da ke Rumuolumeni. Sun samu nasara balle kofan gaban kawai sai yan sanda suka bullo.

Amma, mambobin yan fashin hade da wani dan sanda, Gabriel Igwe, sun arce yanzu. An tabbatar da cewa Ndudiri,ma’aikacin bankin ne ya shirya fashin tare da hadin kan yan sanda.

Hukumar yan sanda ta saki wani jawabi inda tace : “ Mun damke wani Sergeant nay an sanda tare da wani ma’aikacin banki wadanda suka hada bakin domin yin fashi a ranan 23/12/2016 misalin kare 11:35 na safe.

A bangare guda, yan sanda sun dake wani faston Cherubim and Seraphim church of Zion a Legas da wata mata da laifin ajiyewa yan bindiga makamai da kuma yi musu girki.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel