Nakasassheyar yarinya Rahma Haruna wacce ke rayuwa a roba ta mutu (hotuna/bidiyo)

Nakasassheyar yarinya Rahma Haruna wacce ke rayuwa a roba ta mutu (hotuna/bidiyo)

An sanar da mutuwar Rahma Haruna mai shekaru 20, wacce ke rayuwa cikin roba a jihar Kano. Ta rasu a ranar Lahadi, 25 ga watan Disamba.

Nakasassheyar yarinya Rahma Haruna wacce ke rayuwa a roba ta mutu (hotuna/bidiyo)
Nakasassheyar yarinya Rahma Haruna wacce ke rayuwa a roba ta mutu

Wani mutumi mai suna Shamsuddeen Lukman Abubakar ya kai sanarwan shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 26 ga watan Disamba, cewa: “Allah ya ji kan ki Rahma Haruna.”

Rahma ta kasance a cikin roba duk muddin rayuwarta an rahoto cewa kimanin watanni shidda da suka wuce gabbar jikinta ya daina aiki. Labarinta ya yi yawo a yanar gizo a watan Janairu lokacin da mutane suka ga hotonta da kaninta mai shekaru 10 ya dauke ta a cikin roba, cikin tausayawa mutane da dama suka taimaka mata da kudi, kayan sawa, kayayyakin abinci, kujeran guragu da sauran abubuwa.

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: An kai harin kunar bakin wake a Borno

'Yar asalin garin Ladin Makole dake jihar Kano, a baya ta kasance ana dauko ta har cikin birnin Kano ana yin bara da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel