Noman shinkafa: Najeriya ta ciyar da Kamaru, Chadi da Nijar

Noman shinkafa: Najeriya ta ciyar da Kamaru, Chadi da Nijar

Kasar Najeriya, yaya babba a nahiyar Afirka ta sake tabbatar da matsayinta na giwar Afirka sakamakon yadda kasashe makwabtan Najeriya kamar su Nijar, Kamaru da Chadi ke rububin shigowa jihar Kebbi domin siyan shinkafa don kaiwa kasashen su.

Noman shinkafa: Najeriya ta ciyar da Kamaru, Chadi da Nijar

Jaridar Leadership ta ranar Lahadi ta bayyana cewar jihar Kebbi ta zamto wata cibiyar hadahada kasuwancin shinkafa tun bayan samun habbaka aikin noma da gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Atiku Bagudu ke yi tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da babban bankin kasa.

KU KARANTA: Abin da ya sa ba a samu taki bana ba-Ministan noma

Rahoton ya bayyana cewa yan kasuwa daban daban daga kasashen nan uku suna ta kwararowa jihar Kebbi domin yin ciniki, majiyoyin mu sun shaida ma jaridar cewar sama da Tireloli 100 ke fita daga kasuwannin jihar a kowace rana.

Wasu daga cikin shinkafan da suka fi yawa a kasuwannin sun hada da FARO, LABBANA sai kuma sabuwar shinkafa LAKE. Sai dai jama’a da dama suna rokan gwamnati data siya hatsi dayawa ta ajiye, zuwa lokacin da amfanin gona zai ja baya.

Jami’in dake kula da rumbun gwamnatin tarayya a jihar Kebbi Injiniya Suleiman yace rumbunan gwamnati nada girman da zasu tara dubunnan buhuhuwan hatsi da za’a a jiye a cikinsu. Ganin yadda ake zuwa siyan shinkafar Najeriya daga kasashen waje, Shima shugaban kungiyar manoma shinka ta jihar Kebbi Alh Sahabi Augie ya roki gwamnatin tarayya data sanya hannu wajen siya tare da tara shinkafar saboda gaba.

A wani labarin kuma, jaridu da dama sun ruwaito shugaban hukumar kwastam ta kasa reshen jihar Legas Haruma Mamudu yace ya kama buhuhuna 102 na shinkafar roba mai suna ‘Best Tomato Rice’, wanda yace Allah kadai yasan halin da jama’a zasu shiga da an bari ta shigo kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel