Dan Sanda ya shiga buda wuta a Banki a Zaria

Dan Sanda ya shiga buda wuta a Banki a Zaria

– An shiga rudani Jiya a Unguwar PZ da ke Garin Zaria

– Wani Jami’in tsaron wani Banki ya shiga harbi babu gaira-babu dalili

– Wannan abu ya faru ne a Zenith Bank

Dan Sanda ya shiga buda wuta a Banki a Zaria
Dan Sanda ya shiga buda wuta a Banki a Zaria

A Jiya Jumu’a da safe, Mutanen Garin Zariya sun shiga cikin wani rikici. Jama’a da dama dai sun dauka fashi aka yi kokarin yi a Unguwar PZ. An samu takaddama har ta kai ga rashi a wani Banki da ke Unguwar PZ.

Wata Majiya tace wani Jami’in tsaro na Bankin Zenith da ke Unguwar ne ya shiga harbin iska, babu dalili. An bayyana cewa Jami’in da ke tsare da Bankin ya samu ja-in-ja da wani Soja, daga nan kurum ya shiga harbi hagu da dama.

KU KARANTA: EFCC ba ta da amfani inji Balarabe Musa

An ce mutane uku sun rasa rayukan su, ciki akwai dalibin Makaranta. Jami’in da ke tsare da Bakin dai Jami’in Mobile Police ne. Mutane da dama sun dauka fashi aka yi kokarin yi. Sai daga baya da muka leka wurin mun ga abubuwa sun lafa. Amma da alamu an rufe Bankin.

Kwanan nan ne dai aka yaye Sojoji daga Barikin da ke Sabon Garin Zaria. A wancan Asabar din ne wasu kuratan Sojin su ka gama horon na su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel