Launukan jikin Man wanke hakora da manufarsu

Launukan jikin Man wanke hakora da manufarsu

Shin ka taba lura da launukan da ake sawa jikin mazubin man wanke hakora da kuma abinda suke nufi? Ga bayanin dalla-dalla don rigakafi ya fi magani

Launukan jikin Man wanke hakora da manufarsu
Launukan jikin Man wanke hakora na taimaka wajen kula da hakoranka

Man goge hakora na matukar alfanu ga lafiyarmu, sai dai wasu mutanen ba za su iya fadar takamaiman abubuwan da suke amfani da shi don kare lafiyarsu ba, wanda hakan abin mamaki ne matuka.

Kusan kowane mazubi na man goge hakora yana da alama, duk da muna yawan amfani da shi, yawancinmu babu ruwanmu da alamar ballantana mu san abin suke nufi.

KU KARANTA KUMA: Mata ne suka jagoranci kai ma tawaga ta hari – Inji El-Rufai

Idan ka duba man goge hakoran da ka ke amfani da shi, akwai wata alama ta wani launi a karshen gidan man goge hakoran, launin zai iya zama Ja, ko shudi, ko kuma baki.

Wannan launi da ke a kasan man goge hakorar alama ce ta inganci. Wannan shi ne a lokacin da ka gane ainihin abubuwan da aka harhada aka yi man da su; daga nan za ka gane ko an hada ganyeyyaki da tsirai daga noman takin dabbobi, ko kuma da sinadarai na dakin kimiyya aka yi, ko kuma duka biyun.

Launukan da suke kasan mazubin man goge hakoran suna da ma’anoni da yawa kamar haka; Man goge hakoran da ya ke da alamar JA, to an yi shi ne daga gamayyar Sinadari da kuma tsirrai da aka noma da takin dabbobi.

Idan kuma ya kasance da alamar SHUDI ne, to yana nufin akwai abubuwan da aka hada na Allah da annabi, da kuma kwayoyi daga abin da aka hadashi.

Mai alamar KORE kuwa, watau ruwan ganye, na nufin mahadinsa tsirrai ne da itatuwa zalla, yayin da mai alamar BAKI yana dauke ne da Sinadarai zalla.

Lafiyar hakoranmu daidai ta ke da lafiyar jiki baki daya, saboda haka yana da muhimmanci ka san irin man goge hakoran da ka ke amfani da shi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta nesanta kanta daga jerin sunayen jakadu 47

Man goge hakora mai alamar KORE shi yafi dacewa ga lafiyar hakoranka. Amma SHUDI ma za a iya amfani da shi idan babu kore lokaci zuwa lokaci..

Yana da mahimmanci ka rika kula da wadannan alamomin, domin duk lokacin ka canza man goge hakora, to akwai yiwuwar za ka sami canji a hakoranka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel