Gwamnatin Kaduna ta kafa dokar tabaci a wadannan kananan hukumomin

Gwamnatin Kaduna ta kafa dokar tabaci a wadannan kananan hukumomin

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa’i, ya ce kananan hukumomi guda uku na jihar zasu kasance a karkashin dokar hana fita ta tsawon wanni 12, yayin da ake bikin zagayowar Kirsimeti.

Gwamnatin Kaduna ta kafa dokar tabaci a wadannan kananan hukumomin
Gwamnatin Kaduna ta kafa dokar tabaci a wadannan kananan hukumomin

Kananan hukumomin da wannan doka zata shafa sune Kaura, Jema’a da kuma Zangon Kataf da ke kudancin jihar, domin kare yiwuwar tashin rikicin kabilanci a yankunan.

El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa ta dauki matakin ne, sakamakon rikicin da ya barke a farkon sati, a lokacin da wasu daga cikin al’ummar garin Kafanchan da ke kudancin jihar, suka fito domin gudanar da zanga zangar lumana, da nufin kokawa kan hare-hare da suka ce makiyaya na kaimusu a kananan kauyukan da ke yankin.

KU KARANTA KUMA: Bikin Kirismeti: Shugaban Kasa yace a biya Ma’aikata Albashin su

To sai dai kuma a zantawarsa da majiyar mu, wani mazauni a yankin, Injiniya Sa’ad, ya shaida mana cewa, jim kadan da fara zanga zangar sai ta juye zuwa tashin hankali, inda ta kai ga mutanen, sun kone shaguna akalla 8 da Masallaci guda na Hausawa.

Ko da yake Injiniya Sa’ad ya shaida mana cewa babu wanda ya rasa ransa, ya ce akwai wadanda suka samu raunuka.

Tun a waccan lokacin dai rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna ta dauki matakan kwantar da tarzomar, bayan zuwan kwamshinan ‘yan sanda da kuma Gwamnan jihar yankin.

A zantawarsa da manema labarai Gwamna el-Rufa’i, ya sha alwashin hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen kitsa rikicin, da kuma daukar matakan ganin hakan bata sake aukuwa ba.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa da shafin facebook: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel