Wuya-koda-magani-ba dadi! Mayakan Boko Haram na ci gaba da tserewa

Wuya-koda-magani-ba dadi! Mayakan Boko Haram na ci gaba da tserewa

Rundunar sojojin Nigeria ta ce mayakan Boko Haram da dama na ci gaba da tserewa daga maboyar su a dajin Sambisa sakamakon farautar su da dakarun soji ke yi a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Wuya-koda-magani-ba dadi! Mayakan Boko Haram na ci gaba da tserewa
Wuya-koda-magani-ba dadi! Mayakan Boko Haram na ci gaba da tserewa

Kakakin rundunar sojojin kasa ta Nigeria Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya aike wa manema labarai.

Sanarwar ta kuma bukaci al'umma a jihohin Adamawa da Borno da Yobe da su rika sa ido sosai tare da kai rahoto ga jami'an tsaro na duk wani mutum da ba su amince da shi ba.

Rundunar sojin ta sake jaddada cewa ta karya lagon mayakan Boko Haram kuma nan da karshen wannan shekarar dakarun sojin kasar za su kakkabe daukacin ragowar 'yan kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Bacin rana: Damisa ta kai ma Uwar-dakinta hari

A wani labarin kuma, Tafiye tafiyen kasashen wajen da shugaba Buhari da mataimakin sa za suyi a shekara mai kamawa tare kuma da sauran mukarraban su zata lakume kudin Najeriya da suka kai N1.05biliyan.

Sauran tafiye-tafiyen cikin gida kuma zasu lakume zunzurutun kudin da suka kai N353,115miliyan duk a cikin shekarar ta 2017.

Wannan dai yana kunshe ne a cikin daftarin kasafin kudin shekarar ta 2017 da shugaba Buhari ya gabatar a wakonnin da suka gabata a zauren majalisar dake a Abuja.

Ku biyo mu a tuwita @naijcomhausa da shafin fecebook: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel