Bacin rana: Damisa ta kai ma Uwar-dakinta hari

Bacin rana: Damisa ta kai ma Uwar-dakinta hari

Hausawa na cewa Damisa ki sabo! Kwatankwacin haka ne ya faru a kasar Siberia inda wata damisa da ake wasa da ita ta fusata hart a kai ma mai ita hari Lyubov Yakovleva inda ta yaga mata hannu.

Bacin rana: Damisa ta kai ma Uwar-dakinta hari
Damisa ki sabo

Wannan mummunan lamari ya faru ne a lokacin da matar mai shekaru 53 ke wasa da damisar a dakin wasa na Bogotol, dake yankin Krasnoyarsk a kasar Siberia tare da danta Tim Uskova mai shekaru 4.

KU KARANTA: An yi ma barayin Bunsuru horo mai tsanani a kasar Kenya

Matar tace “ana cikin wasa kwatsam sai damisar ta fado min a gabana, nan da nan na kare Tim, kawai sai ta fara cizo na tana yaga min fata, kafin kace wani abu mutane duk sun tsere”

Bacin rana: Damisa ta kai ma Uwar-dakinta hari
Uwar dakin damisar,Lyubov Yakovleva

Sai dai abinka da Turawa, nan da nan aka garzaya da ita zuwa asibiti bayan ma’aikatan gidan wasan sun kama Damisar, sun rufe ta.

Jaridar Siberia Times ta bayyana cewar da fari matar ta fitar da Damisar mai suna (Loki) daga filin wasan bayan ta fahimci ta fara fusata, amma sai ga shi ana dawo da ita sai ta far ma mai ita. Anyi ma matar dinki a wurare 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel