Hoton bidiyon Dan Sanda na fada da direba ya janyo ka-ce-na-ce

Hoton bidiyon Dan Sanda na fada da direba ya janyo ka-ce-na-ce

- Wani dan sanda yayi kokawa da Direba kan cin hancin Naira 500 a Unguwar Ikorodu ta Jihar Lagos, wani kuma ya dauki hoton bidiyon ya kuma sa intanet da hakan ya janyo ka-ce-na-ce

- A yayin kokawar dan sandan ya yar da bindigarsa kuma wasu sun dauka, har yanzu ba'a kai ga gano da dan sandan ba

Hoton bidiyon Dan Sanda na fada da direba ya janyo ka-ce-na-ce
Hoton bidiyon Dan Sanda na fada da direba ya janyo ka-ce-na-ce

Wani jami'in dan sanda da har yanzu ba a kai ga gano shi ba, ya shiga tasku bayan da aka dauki hoton bidiyonsa yana kokawa da wani direban babbar mota a unguwar Odogunyan ta Ikorodu da ke jihar Lagos, kan cin hancin Naira 500.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata a kashe EFCC-Kungiyar CNPP

A yayin kokawar, bindigar dan sandan ta fadi a lokacin da ya ke kokarin yin tsalle ya shiga motar, wani kuma daga cikin abokan direban ya dauke, ya kuma gudu da ita.

Mutumin da ke daukar bidiyon an jiyo shi yana ta maimaita "baka da hankali", yayin da wani daga bayansa aka jiwo shi yana cewa, "Dauki bidiyonsa! gudu da bindigar! kai sha-sha-shan dan sanda ne, an dauke ka a waya, kashin ka ya bushe!"

Mai daukar bidiyon na fadin, "Kai wawa ne! korar ka za a yi, ba ka da tunani."

Wani kuma daga cikin ‘yan kallo cewa ya ke, "Wannan shine karo na biyu da yake irin haka; kwanakin baya ma haka yayi fada da wani mutum."

Jaridar The Punch, ta rawaito wanda yasa bidiyon a Facebook mai suna, Mc Gabito D'laffgiva, kuma al-amarin ya faru ne akan cin hancin Naira 500 da dan sanda ya nema daga hanun direban.

D'laffgiva yace, "dan sandan maras ta-ido, ya kama kokawa ne da direban wanda ke dauke da lodin tarkace bayan da ya nemi cin hancin Naira 500 daga gareshi. A kan idona hakan ta faru akan titin Odo Nla, Odogunyan."

Har lokacin hada wannan labari, D'laffgiva bai amsa bukatar wakilin mu ta neman karin bayani ba.

Sai dai, wasu daga cikin wadanda suka yi tsokaci kan labarin sun zargi D'laffgiva da bada gudun-mawa wajen cin zarafin dan sanda.

Wani mai suna Fayanju Ayokunle yace, "kun daki dan sanda, kun gudu da bindigarsa, amma duk da haka kake da jarumtar yadawa a yanar gizo-gizo…. wadannan mutane sun ji kunya da suka daki dan sanda; ku kuma kunji kunya da kuke yanke hukunci ba tare da jin daya bangaren ba."

Wani kuma mai suna Dele Aina, cewa ya ke yi, "lallai wannan dan sanda bata-gari ne amma ku kuma masu fada da dan sandan da ke dauke da bindigar AK-47, ku ne ku ka fi kowa wauta a duniya!"

KU KARANTA KUMA: Ana shirin maido Ibori Najeriya

Da ya ke mayar da martani, D'laffgiva sa yace "Bai kamata a zargi direban da abokan sa ba…. Kawai dai na tsaya ne ina kallon yanda sha-sha-shan dan sanda cikin rashin sanin mutuncin kai ke fada da direba gaban duk jama'a akan biyan bukatar san rai.

Yayin da wakilin mu ya tuntubi mai magana da yawun "yan sandar jihar, SP Dolapo Badmos, tace bata da masaniya faruwar lamarin har ya zuwa wancan lokaci. Ta kara da cewa zata tuntube mu sanda ya dace.

Aiko da ra’ayinku dangane da wannan labari a shafinmu na Tuwita @naijcomhausa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel