Sojoji na cin bakar wuya a Sambisa

Sojoji na cin bakar wuya a Sambisa

A ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2016 ne a ka fitar da wani hoton bidiyo da ke nuna irin bakar wahalar da sojoji ke sha a yakin da suke yi da ‘yan ta’addan Boko Haram a dajin Sambis saboda karancin abinci da ruwan sha

Sojoji na cin bakar wuya a Sambisa
Sojoji na cin bakar wuya a Sambisa

Hoton bidyon na nuna yadda wani jirgi mai saukar ungulu mai dauke da ruwa, da abinci ga sojojin masu fama da yunwa bai gama suka ba, aka rufar masa da wawa.

Sojojin dai sun kasa jiran jirgin ya gama sauka, matukin kuma ya kintsa, a kuma rarraba abincin a gare kafin su daka wasoso.

KU KARANTA KUMA: An yi ma barayin Bunsuru horo mai tsanani a kasar Kenya

A farkon makon nan dai, da akwai wani hoton bidiyon na sojojin da aka yi ta yadawa intanet, a inda aka nuna su suna fada da ‘yan ta’adda a kauyen Alagarno.

An ga wasu daga cikin sojojin na yi wa ‘yan uwansu wadanda ko suka suma, ko kuma matukar gajiya ta sa sun galabaita an yi musu fifita.

Sai dai Kakakin rudunar sojin Sani Usman Kukasheka ya ce, ba haka batun yake ba, kuma wasu batagari ne suka yi hoton bidiyon domin sharri, hakan a cewarsa, ba ya nuna ainihin halin da sojojin suke ciki a yanki.

A wani labarin kuma Babban Hafsan sojojin Janar Burutai ya aikawa da sojojin da ke bakin daga da wata kyauta ta musamman a mtsayin goron Kirisimeti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel