Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)

Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)

- Rahotannin da ke yawo suna nuna cewar wasu bata gari daga kasar Sin watau China sun fara cika kasuwannin kasashen Afrika ciki kuwa hadda Najeriya da wata samfurin shinkafar bogi ta roba

- Ita dai kasar ta Sin ta yi kaurin suna wajen samar da kayayyakin anfani na bogi ciki kuwa hadda kayayyakin abinci

Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)
Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)
Asali: Depositphotos

Tun farko dai wata jaridar kasar Korea ce ta fara bankado labarin na wasu yan kasar China din da ke kera shinkafar roba kuma tuni har sun fara rarraba ta a kasashen duniya musamman ma a Afrika.

Ga wasu hanyoyi nan har guda 6 da amintaccen kamfanin jaridar nan taku na Legit.ng ya zakulo maku don anfanin kawunan mu kan hanyar da za'a bi wajen gane shinkafar ta boji. Gasu a kasa:

1. Hanyar turmi da tabarya

Idan ku ka samu shinkafar ku sai ku dan daka ta a cikin turmi da tabarya, idan har ta dan yi farin gari to tabbas wannan shinkafar ta kwarai ce mai kyau amma idan kuka ga wani koriyar kala tana fita daga gare ta to tabbas shinkafar bogi ce. Sai a kiyaye.

2. Gwaji da wuta

Ai ina fata dai duk munsan yadda kaurin roba yake idan ana kona ta ko? To hakan ne ma ake yin wannan kwagin. Idan kuka samu shinkafar sai a nan kona ta, idan har ta kama da wuta kuma aka ji kaurin to tabbas tanan ma za a iya tantancewa.

Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)
Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)

3. Gwaji a cikin ruwa

Idan muka samu kofi da ruwa a ciki sai a nan dibi shinkafar da ake kokwanto a zuba a cikin kofin. Idan har shinkafar ta nutse a cikin ruwan to tabbas tana da kyau da inganci, idan kuwa akasin haka ya faru to tabbas ta bogi ce.

4. Gwajin dambada

Yadda ake wannan gwajin kuma shine a samu shinkafar da ake kokwanto sai a dan dafa ta kadan sai a tsameta abarta a wani wuri mai lema ta kwana kamar 2 zuwa 3. Idan har tayi hunhuna to tana da kyau kenan.

5. Ta hanyar tafasawa

Idan ana tafasa shinkafar da ake kokwanton sai a kula da irin kumfan da ke fita a jikin tukunyar. Idan har kuka ga kumfan da takeyi ya wuce misali, to tabbas shinkafar ta bogi ce.

Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)
Shinkafar roba ya watsu a kasuwannin Najeriya: Ga hanyoyi shida da zaka gane ta (Karanta)

6. Gwaji ta hanyar tafasashen mai

Sai a samu shinkafar da ake kokwanton ingancin ta sai a samu tafasasshen mai a zuba shinkafar a ciki. Idan har ta roba ce to za kuga ta fara narkewa sannan kuma tana hadewa da juna. Idan har hakan ta faru, sai a kiyaye, shinkafar ta bogi ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel