Yaki da rashawa: Babu shafaffe da mai a gwamnati ta -Buhari

Yaki da rashawa: Babu shafaffe da mai a gwamnati ta -Buhari

Biyo bayan umurnin da Shugaba Buhari ya baiwa ministan shari'a na cewa ya binciki minstocinsa, wasu 'yan Najeriya na ganin ba da gaske gwamnati ta keyi ba saboda wadanda ake korafi a kansu na hannun damansa ne.

Akwai wasu 'yan Najeriya ma da suke ganin minstan shari'a da shugaban kasa ya umurceshi ya yai aikin bashi da hurumi ko matsaya a hukumance yayi aikin kuma wadanda zai bincika su ma ministoci ne.

Yaki da rashawa: Babu shafaffe da mai a gwamnati ta -Buhari
Yaki da rashawa: Babu shafaffe da mai a gwamnati ta -Buhari

Gwamnatin Buhari ta mayarda martani da lafazi mai kaifi akan wadanda suke nuna shakku da kuma yin tababan gaskiyar gwamnatin. A cewar mutanen kokari a keyi a yi rufa rufa a yi yiwa mutane boko ko dodorido.

Amma kakakin fadar shugaba Buhari, Malam Garba Shehu yace lokacin da suka fitar da sanarwa basu amabaci sunan kowane minista ba. Harsashe ne na mutane har suna zayyana wasu sunaye.

KU KARANTA KUMA: Sultan Abubakar ya kai ma gwamna Fayose ziyara

Yace magana ta yaki da cin hanci da rashawa da gaske a keyi. Babu sani babu sabo. Ko musulmi ko kirista duk wanda aka samu yana aikata ba daidai ba za'a hukumtashi.

Akan atoni janar na kasar yace a duba tsarin mulkin kasa da dokoki. Yana da hurumin ya binciki kowa. Yayi misali da Amurka inda atoni janar ta binciki Bill Clinton yana shugaban kasa a lokacin akan harkarsa da Monica Lewinski. Shi ya nadata amma tayi babu sani babu sabo. Haka ma ya faru a Israila.

Babban lauyan gwamnati ya san ikon da yake dashi a maganar saboda haka duk duniya ta sa masa ido ya je yayi abun da zai yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel