Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan laraba

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan laraba

Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman batutuwan da suka auku afadin Najeriya a jiya laraba, 21 ga watan Disamba, 2016.

1. Babban lauyan Najeriya ya fara bincikan Ibrahim Magu

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana
Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana

Duk da kokari da shure-shure na hana bincikan zargin da ake wa shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ,Ibrahim Magu, babban lauyan tarayya kuma ministan Shari’a,Abubakar Malami, ya fara bincike cikin zargin da akewa Magu bisa ga umurnin shugaba Muhammadu Buhari.

2. Yan Najeriya sun tura kudi $35 zuwa gida daga waje cikin 2016

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana
Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana

Game da cewar jakadan kungiyar shiga da faita ta duniya wato International Organisation for Migration (IOM), Enira Krdzalic, kudaden da aka turo Najeriya daga kasashen waje ya kai $35 million a 2016.

3. Hukumar Sojin Najeriya zata bude filayen kiwo a fadin kasa

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana
Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana

Hukumar Sojin Najeriya zata bude filayen kiwo a fadin kasa. Wannan labari ya bayyana ne daga bakin Manjo Janar Patrick Akem,a ranan Talata 20 ga watan Disamba,a taron kaddamar da kasuwar Mammy a barikin sojoji da Abuja.

4. Yan majalisar kasar Ingila sun kalubalanci Buhari akan Biafra

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana
Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana

Yan majalisan dokokin kasar Ingila 16 sun umurci ofishin jakadan Ingila a Najeriya ta kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari akan tsare Nnamdi Kanu

5. Kuyi hattara da zumar da ake shigowa da shi Najeriya daga waje- Gwamnatin tarayya

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana
Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana

Cif Audu Ogbeh, ministan aikin noma da raya karkara ya bayar da gargadi ga yan Najeriya akan kasancewan zuman jabu da ake shigowa da shi Najeriya

6. Zan cigaba da aiki domin hadin ka Najeriya

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana
Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yace zai cigaba da tabbatar da hadin kan kasarmu Najeriya. Yayinda yake Magana a wata taro a Owerri , Obasanjo yace cigaban Najeriya nada muhimmanci a garesa.

7. An saki James Ibori daga kurkuku a Ingila

Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana
Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan lantana

Wata kotun kasar Ingila ta bayar da umurnin sakin tsohon gwamnan jihar Delta, James Onanefe Iboridaga gidan yari a yau laraba21 ga watan Disamba.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel