Za a inganta harkar hako ma’adanai a Najeriya

Za a inganta harkar hako ma’adanai a Najeriya

– Gwanatin tarayya na shirin inganta harkar hako ma’adinai na Kasa

– Gwamnati ta samo kudi har Dala Miliyan $150 daga Bankin Duniya

– Najeriya na shirin daina dora hannayen ta biyu kan man fetur

Za a inganta harkar hako ma’adanai a Najeriya
Za a inganta harkar hako ma’adanai a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta samo kudi har Dala Miliyan $150 daga Bankin Duniya domin inganta shirin hako ma’adinan cikin Kasa. Gwamnatin Kasar na kokari rage dogoran da aka yi kan man fetur zalla.

Ministan Ma’adanai na Kasar, Dr. Kayode Fayemi ya bayyana haka a farkon makon nan. Minista Fayemi yayi wannan jawabi ne da manema labarai a Abuja. Yace an samu wannan makudan kudi daga hannun Bakin Duniya.

KU KARANTA: Gwamna yayi kaca-kaca da EFCC

Dr. Kayode Fayemi yace Ma’aikatar na kuma kokarin tara kudi har dala Miliyan $600 daga wasu asusu na Kasar domin Inganta sha’anin hako ma’adan cikin Kasa. Yace zuwa tsakiyar badi ana sa ran a samu wannan kudi.

Za dai ayi amfani da kudin da aka samu daga Babban Bankin Duniya ne domin tallafawa gidauniyar harkar hako ma’adinan Kasa ne. Fayemi yace hakan zai taimakawa kananan masu hako arziki daga cikin Kasa. Najeriya dai tana da arziki da dama cikin Kasa, sai dai Kasar ta dogara ne gaba daya kan Man Fetur wanda yanzu farashin sa yayi kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel