An amince Jami’ar A.B.U ta gina makarantar koyon kasuwanci

An amince Jami’ar A.B.U ta gina makarantar koyon kasuwanci

– Jami’ar ABU ta Zaria za ta gina Makarantar koyon kasuwanci

– Majalisar Jami’ar ta bada damar ayi wannan aiki

– Akwai irin wannan Makarantar tuni a Legas

An amince Jami’ar A.B.U ta gina makarantar koyon kasuwanci
An amince Jami’ar A.B.U ta gina makarantar koyon kasuwanci

Jami’ar Ahmadu Bello watau ABU Zaria za ta bude Makarantar koyon kasuwanci. Majalisar Jami’ar ta amince a bude wannan Makaranta kamar yadda Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana.

Farfesa Ibrahim Garba ne yayi wannan bayani a Jiya wajen bikin gina wani Dakin taro mai daukar mutane 300 a Jami’ar. Kungiyar ICAN ta kwarararrun Akawu na Kasar ce za ta gina wannan dakin karatu.

KU KARANTA: Kwastam tayi wani kamu

Idan har an bude Makarantar Koyon kasuwancin, za a rika koyar da Ilmin Tattali da akawu da Ilmin kasuwanci har da ma Ilmin Banki na Musulunci da sauran su. Farfesa Garba yace Makarantar za ta rika bada shaidar Digirgir da Digir-digir da ma Diploma. Dama can akwai irin wannan Makaranta a Jihar Legas.

Kwanakin baya Jami’ar ta yaye dalibai masu digiri guda 11, 731. Kamar yadda muka samu labari akwai guda 2, 697 masu shaidar Digiri na biyu, sannan kuma guda 289 sun kammala karatun Digiri na uku. Akwai kusan 50 masu Digiri mai makin farko watau first class. Jami’ar Ahmadu Bello dai ita ce ta farko a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel