Allah wadai! Jiga jigan yan siyasa sunyi dambe akan yan mata

Allah wadai! Jiga jigan yan siyasa sunyi dambe akan yan mata

Wasu jiga jigan yan siyasa a kasar Kenya sun dambace a bainar jama’a akan kudin kungiyar mata.

Allah wadai! Jiga jigan yan siyasa sunyi dambe akan yan mata
Allah wadai! Jiga jigan yan siyasa sunyi dambe akan yan mata

Yan siyasan da aka bayyana sunayesu sun hada da Justus Kibaba da dan takarar majalisa Didmus Barasa dukkaninsu yan jam’iyyar Jubilee sun yi fadar ne a ranar bikin Jamhuri a filin wasa na Amtalla ranar Litinin 12 ga watan Disamba.

Rikicin ya samo asali ne tun bayan da Barasa ya zargi Kibaba da karkatar da kudaden daya bashi don ya baiwa kungiyar matan jam’iyyar tasu, inda Barasa yace ya baiwa Kibaba posho miliyan 12 don ya raba ma mata talakawa, amma sai Kibaba yaje ya baiwa yan matansa.

KU KARANTA:Shugaba Buhari ya karɓi bakoncin zaɓaɓben shugaban kasar Ghana mai jiran gado

“na baka umarnin ka raba ma mata marasa karfi talakawa kudi har posho miliyan 12, amma sai kaje ka ware wasu yan matanka ka raba musu kadai” inji Barasa.

Sa’annan Barasa ya sake nanata zargin da ake yi ma Kibba na cinye tsabar kudi posho miliyan 3 da aka ware don siyan ma mata injin kyankyasan kwai.

Sai dai wani shedan gani da ido wanda lamarin ya faru a gaban shi yace lokacin da Kibaba ya harzuka, sai ya hayo kan dakalin jawabi, inda ya kwace na’urar yin magana daga hannun Barasa. Kafin kace kule! Yan siyasan sun kaure da fada, ko kafin a rabasu tuni sun yayyaga ma juna riga tare da jima juna ciwo.

Suma yan siyasan Najeriya ba’a barsu a baya ba wajen fada, kalla a nan:

Asali: Legit.ng

Online view pixel