Jami'an Kwastam sun kama shinkafar roba a Lagos

Jami'an Kwastam sun kama shinkafar roba a Lagos

-Jami’an Hukumar Kwastam sun kama buhunan shinkafa ‘yar jabu da aka yi ta roba, ake kuma kokarin sayarwa jama’a a bikin Krisimeti

- An kuma samu nasarar damke wani da ake zargin yana da hannu da shigo da shinkafar mai illa ga lafiyar jama’a idan aka yi amfani da ita

Jami'an Kwastam sun kama shinkafar roba a Lagos
Jami'an Kwastam sun kama shinkafar roba a Lagos

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa, Kwastam, ta kama buhunhuna 102 na wata shinkafa da ake zargin ta roba ce, yayin da masu fasan kwabri su ka yi yunkurin shigar da ita cikin kasuwanni domin sayarwa da jama'a.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, ya rawaito cewa, reshen Hukumar da ke Ikeja ne yayi nasarar kama nau'in shinkafar mai suna "Beat Tomato Rice" wacce ba ta da shaidar kwanan watan da aka yi ta.

Shugaban hukumar na yankin, mai suna Mohammad Haruna ne ya bayyana a hakan a ranar Talata 20 ga watan Disamba na shekarar 2016, ya kuma ce, an boye shinkafar ne domin sayarwa jama’a a lokacin bukin Kirsimeti.

Haruna ya kuma ce, jami'an hukumar sun kama shinkafar ne a ranar Litinin a Ikeja kuma sun damke wani da ake zargin yana da alaka da haramtacciyar shinkafar.

Ya ce: "Kafin wannan lokaci na yi zaton jita-jita ne kawai cewar shinkafar ta yadu a duk fadin kasar nan, amma da wannan kame, na tabbata cewa lallai akwai irin wannan shinkafar. Mun gabatar da bincike na kusa-kusa akan shinkafar. Bayan dafa ta mun tabbatar tana da illa kuma Allah ne kadai yasan mai zai faru da jama'a sun ci”.

“Don haka ina gargadin irin wadannan masu neman duniya ta kowanne hali, wanda suke ganin wannan lokaci na Kirsimeti a matsayin lokacin da za su ci karensu babu babbaka, da su nisanci irin wannan kasuwancin”.

Babban Jami’in Kwastam din ya kuma ce, jami’an hukumar na kokarin toshe duk wata kafa ta shigo da irin wannan shinkafar tare da sayar da ita ga jama’a.

Wacce suka kama kuwa, za su mika ta ne ga Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, don ci gaba da zurfafa bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel