Inyamuri da dan Arewa abokan juna ne –Sarkin Musulmi

Inyamuri da dan Arewa abokan juna ne –Sarkin Musulmi

- Shugaban al’ummar Musulmai a Najeriya ya ce ‘yan Arewa ba su tsani ‘yan kabilar Igbo ba, ba kuma su suke kashe su ba illa barayi masu ta da zaune tsaye

- Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ba za a kawo karshen kashe-kashe ba a kasar sai ‘yan Najeriya sun dunkunle sun yaki lamarin tare da jami’an tsaro

Inyamuri da dan Arewa abokan juna ne –Sarkin Musulmi
Inyamuri da dan Arewa abokan juna ne –Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce babu wani shiri da ke yin na hallaka ‘yan kabilar Ibo da ke zaune a arewancin kasar.

Shugaban al’ummar Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin wata liyafar girmamawa da aka yi masa a garin Nsuka ta jihar Enugu a ranar Talata 20 ga watan Disamba na shekarar 2016.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, Sarkin na Musulmi wanda kuma shine Sultan na Sakkwato, ya bayyana cewa, kasancewar ‘yan kabilar ta Ibo a kowanne lungu da sako na kasar shi ya sa masu laifi samun damar kai musu hari a ko da yaushe aka samu wata hatsaniya domin sace dukiyarsu.

Sarkin ya kuma ce, Fulani makiyaya na ainihi ba su da hannu cikin wadannan kashe-kashen da ake yi a kasar kamar yadda ake ta yadawa. Ya ce, wasu masu son aikata laifi ne suke shiga rigar Fulanin suke kuma tafka barna.

Mai alfarma Sarkin ya yi kira ga jami'an tsaro da su yi aikinsu tare da binciko masu kisan,

Ya kuma ce: "Ina mai shaida muku cewa, babu wani mutumin Arewa da ya ke nufin kashe wani dan kabilar Igbo kawai dan kasancewar sa Igbo.

“Ana kashesu ne dan sune kawai domin su ne jajirtattun mutanen da ake samu a ko ina, a kowane kauye amma ba wani da ke shirya kisan ko aikawa a kashe Igbo."

Tun da fari, Sarkin ya bayyana cewa, wasu Fulani na zaune na tsawon lokaci tare da ‘yan kabilar Igbo, saboda haka babu yadda a rana tsaka za su juye su dinga kashe su.

Ya kuma kara da cewa, kamata ya yi duk wanda ya yi kisa a bayyana shi a matsayin mai kisan kai.

“Irin wannan mutum ya kamata a kalle shi a mai kisan kai ko Bafulatani ne ko Igbo, In dai ba mun kalle su a matsayin masu kisa ba, ba zamu iya kawar da wannan ta'annati ba.

“Mun zauna da Fulani na tsawon shekaru, da yawansu ba su san ko ina ba sai kasar Igbo. Shin abu ne mai yiwuwa a ce wadannan mutanen su dauki makami su dinga kashe mutanen da suke tare da su na tsawon lokaci?”

Basaraken ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya kan yadda za’a shawo kan wannan lamari, “Aikinmu ne mu duka mu bankado wadannan masu laifi, aikinmu ne mu duka mu tabbatar cewa sun fuskanci fushin hukuma.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel