Fasaha: Kalli abin mamakin da wani dalibi yayi da kwalaben Coca-Cola

Fasaha: Kalli abin mamakin da wani dalibi yayi da kwalaben Coca-Cola

Bincike ya nuna cewa akwai dimbin hazikan yara masu fasaha a nahiyar Afirka musamman a nan gida Najeriya, da alamu ire iren yaran nan masu basira ba zasu kare ba ma.

Fasaha:Kalli abin mamakin da wani dalibi yayi da kwalaben Coca-Cola

A yau mun ci karo da wani yaro ne, dalibin kwalejin kimiyya da fasaha dake garin Yaba na jihar Legas wanda ya hada wasu abubuwan ban mamaki da ban sha’awa da kwalaban lemun Coca-Cola.

Shi dai dalibin na daya daga cikin yaran da suka shiga gasar da kamfanin Coca Cola ta shirya mai taken ‘gasar kwalbar Coca Cola’, manufar gasar shine don zakulo basirar tunani daga cikin matansan mu, inda ake bukatar su kera ko hada wani abu da za’a kale shi ta fuskoki uku da kwalaben Coca Cola.

KU KARANTA:Uba ya ƙona ýaýansa da karfen wuta akan satar kifi

Wannan gasa an yi shi ne musamman kawai don dalibai na tsangayar zane da abubuwan da suka shafi zane. Wannan wata hanya ce na nuna muhimmancin maimaita amfani da kwalabe da kuma yadda hakan ka iya samar ma matasan mu ayyukan yi. Wasu daga cikin abubuwan da matasan suka hada sun watsu a kafafen sadarwa na zamani, ga kada daga cikinsu:

Fasaha:Kalli abin mamakin da wani dalibi yayi da kwalaben Coca-Cola
Fasaha:Kalli abin mamakin da wani dalibi yayi da kwalaben Coca-Cola

Fasaha:Kalli abin mamakin da wani dalibi yayi da kwalaben Coca-Cola
Fasaha:Kalli abin mamakin da wani dalibi yayi da kwalaben Coca-Cola

Wannan ba shine karo na farko ba da Legit.ng ke watsa labarai irin na wadannan yara masu kaifin basira, idan ba’a manta ba kimanin watanni 9 da suka gabata, Legit.ng ta ziyarci wani fasihin yaro mai suna Oregun Olumide wanda ya kammala karatunsa a YABATECH da digiri mai daraja ta daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel