Yan Najeriya su tura kudi $35 million zuwa gida daga waje cikin 2016

Yan Najeriya su tura kudi $35 million zuwa gida daga waje cikin 2016

- Najeriya ce kasa ta 5 a duniya na kasashen da ake turo kudi cikinta

- A shekarar 2016 kadai, an tura kudi $35 million zuwa Najeriya

Yan Najeriya su tura kudi $35 zuwa gida daga waje cikin 2016
Yan Najeriya su tura kudi $35 zuwa gida daga waje cikin 2016

Game da cewar jakadan kungiyar shiga da faita ta duniya wato International Organisation for Migration (IOM), Enira Krdzalic, kudaden da aka turo Najeriya daga kasashen waje ya kai $35 million a 2016.

Yayinda yake Magana a rana Talata, 20 ga watan Disamba, a taron tattauna ta shiga da fice a Abuja domin bikin zagayowar ranan masu shiga da fice, Krdzalic yace game da rahoton bankin duniya, an samu Karin kudin da ake turowa Najeriya daga $21 million a 2015 zuwa $35 million a 2016.

KU KARANTA: Kasar Jamus ta bada gudunmuwarta ga Najeriya

Game da cewar ta, Najeriya ce kasa ta biyu a Afrika kuma ta 5 a fadin duniya na mutanen kasan da ke waje suna turo kudi gida da iyalai,dangi da abokan arziki.

Tace: game da rahoton bankin duniya, tura kudi ya kuwa ninkuwa sau 3 fiye yadda akeyi da . yana karuwa da kasi 8 cikin dri kowani shekara daga shekara 2013 zuwa 2016.

Kana ta jaddada cewa shiga da fice bas hi da wani illa ga kasashe amma tanada amfani idan aka yi shi yadda ya kamata.

A taron, ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambzzau, yace shiga da fice ba laifi bane , bal ma tana da amfani da haduwar kan kasashe da kuma cigaban su. Amma tana iya zama illa ne idan aka yi shi ba bisa ga doka ba.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel