An samu abubuwa a cikin gidan Alex Badeh

An samu abubuwa a cikin gidan Alex Badeh

– Wani daga cikin mai ba Shugaban Kasa shawara yace gwamnatin tarayya za ta saka ma’aikatan gwamnati a cikin gidan Alex Badeh

– Tolu Ogunlesi yace karamin daki na cikin gidan ya fi mafi yawan gidaje

– Alex Badeh ya rike Shugaban Hafsun Soji lokacin Shugaba Jonathan Goodluck

An samu abubuwa a cikin gidan Alex Badeh
An samu abubuwa a cikin gidan Alex Badeh

Tsohon shugaban hafsun sojin kasar nan Alex Badeh yana da wani wurin rawa a cikin Gidan sa irin wanda ‘yan matan bariki ke zuwa su taka. Wani daga cikin mai ba Shugaban Kasa shawara, Tolu Ogunlesi ya bayyana haka.

Tolu Ogunlesi yayi wannan bayanai ne ta shafin sa na Twitter inda yace Gwamnati ta karbe Gidan Tsohon Shugaban Sojojin Kasar. Yace Gwamnati za tayi amfani da wannan makeken Gidan wajen kamawa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya; hakan zai rage tsada da yawan kudin da ake kashewa.

KU KARANTA: Jamus za ta taimakawa Najeriya

Ogunlesi yace daya daga cikin dakunan gidan ya fi wasu gidajen da dama girma. Sannan yake cewa wani daga cikin dakin kuwa ko Sarauniyar Kasar Philipinees ta zo, sai ta saki baki. A can Kasa kuwa akwai Gidan rawa inda ake tara matan banza.

Hukumar EFCC ce dai ta karbe Gidan tsohon shugaban hafsun sojin Kasar. Ana nan ana ta shari’a yanzu haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel