El-Rufai ya nada mai maye gurbin Hadiza Bala Usman

El-Rufai ya nada mai maye gurbin Hadiza Bala Usman

- Gwamna Nasir El-Rufai ya nada Muhammad Bashir Sa’idu a matsayin shugaban gidan gwamnatin jihar Kaduna

- Saidu ya kasance kwamishanan kanan hukumomi ne kafin wannan sabuwar nadi

El-Rufai ya nada mai maye gurbin Hadiza Bala Usman
El-Rufai ya nada mai maye gurbin Hadiza Bala Usman

Gwamna Nasir El-Rufai na jihae Kaduna ya nada Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Kaduna, Leaderdhip ta bada rahoto.

Mai Magana da yawun gwamna El-Rufai,Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a ranan Litinin ,19 ga watan Disamba.

Game da jawabin, Saidu zai maye gurbin HadizaBala-Usman ,wacce take kujeran kafin shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta a matsayin Dirakta manajan hukumar tashan jiragen ruwan Najeriya.

KU KARANTA: Ibrahim Magu na karkashin madubin DSS

Kafin wannan lokaci, Sa’idu ya kasance kwamishanan kananan hukumomi ne a jihar Kaduna.

Sa’idu akawu ne kuma an haife shi ranan 21 Yuli ,1957 . yananda digir-gir a Business Administration (MBA).

Sa’idu yay aiki da gwamnatin jihar kafin ya koma aiki da hukumar National Maritime Authority (NMA).

Ya kasance dan siyasa wanda mamban tsohuwar jam’iyyar Yar’adua Social Democratic Party (SDP).

Ya rike kujeran mataimakin shugaban jam’iyyar CPC ta kasa kafin jam’iyyar tayi maja ta zamo APC.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel