Gandujen aiki? Za'a gina hanyar jirgin kasa Kano

Gandujen aiki? Za'a gina hanyar jirgin kasa Kano

Gwamnatin jihar Kano a Nigeria, ta kare matakin da ta dauka na bayar da kwangilar shimfida hanyar jiragen kasa na zirga-zirga a cikin gari, da za a yi a kan kudi kimanin dala biliyan daya da miliyan dari takwas.

Gandujen aiki? Za'a gina hanyar jirgin kasa Kano
Gandujen aiki? Za'a gina hanyar jirgin kasa Kano

A kwanakin baya ne gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu akan yarjejeniyar shimfida layin dogon da wani kamfani na kasar China, lokacin da ya kai wata ziyara kasar.

Sai dai wasu mutane a jihar sun soki matakin suna masu zargin cewa gwamnatin na shirin karawa jihar bashi ne kawai.

A yayin wata ziyara da ya kai ofishinmu na London, Sakataren Gwamnatin Jihar Kanon, Alhaji Usman Alhaji ya shaida wa Haruna Shehu Marabar Jos cewa aikin gina layin dogon, wani bangare ne na yunkurin gwamnatin jihar na janyo ra'ayin masu zuba jari.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel