Ina kwanciya da kananan yara ne don inyi arziki – Inji wani Inyamuri

Ina kwanciya da kananan yara ne don inyi arziki – Inji wani Inyamuri

A ranar Asabar 11 ga watan Disamba ne jami’an yansandan jihar Enugu suka cika hannu da wani mutum dake kwanciya da kananan yara don yin tsafin samun kudi.

Ina kwanciya da kananan yara ne don inyi arziki – Inji wani Inyamuri
Mutumin dake kwanciya da yara

Jaridar Souther City ta bayyana cewar mutumin dan asalin kauyen Enugu-Ezike dake karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa ne. sa’annan yansanda sunce wasu daga cikin yara 11 da mutumin ya kwanta dasu yan shekaru 3, 4, 7, 8, 9 da 11.

KU KARANTA:Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 24 a jihar Taraba

Sai dai yansandan sunce mutumin sai yayi musu tsafi tukunna sa’annan yake kwanciya da yaran.

Yayin dayake jawabi, Kaakakin rundunar yansandan jihar Mbere Amaraizu ya bayyana cewar mutumin na amfani da farin kyalle da wani boka ya bashi, inda yake rufe musu fuska, daga bisani sai ya kwanta dasu.

Sai dai kash! Mutumin bai yi arziki ba har aka kama shi!

Zaku iya bibiya labaran mu a nan, ko a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel