Uba ya ƙona ýaýansa da karfen wuta akan satar kifi

Uba ya ƙona ýaýansa da karfen wuta akan satar kifi

Jami’an rundunar tsaron farin kaya (NSCDC) sun kama wani mutum a garin Akure mai suna Alh Kasali saboda cin zarafin yara kanana da aka kama shi yana yi.

Uba ya ƙona ýaýansa da karfen wuta akan satar kifi
Maryam da kaninta Ojonla

Rahotanni sun bayyana cewar Kasali ya kona yaran ne ta hanyar amfani da wata wuka bayan ya sanya wukar a cikin wuta, da wukan ya dau zafi ne sai ya manna ma yarsa Maryam a cikinta, sa’annan ya maimaita hakan akan kaninta Ojonla mai shekaru 6 saboda amaryarsa ta fada mai cewar yaran ne suka sace kifin daya siyo, don haka ne ma yaci miyan tuwonsa ba kifi.

KU KARANTA:Yaro ya ƙera jirgin sama mai tashin Angulu a jihar

Sai dai Maryam tace Ojonla ne ya dan ci wani bangare na kifin, yayin da ita kuma amaryar mahaifin tasu ta cinye sauran kifin, amma sai amaryar ta musanta batun tace ai maryam ne da kaninta suka cinye kifin gaba daya. wannan ne ya harzuka Kasali, har yasa ya yanke wannan mummunan hukunci.

Makwabtan Alh Kasali ne suka rankaya suka kira jami’an hukumar tsaron farin kaya bayan sun tayi mai magiya daya rangwanta ma yaran, amma Kasali yayi kunnen uwar shegu dasu.

Sai dai daga karshe an garzaya da yaran zuwa asibitin gwamnati, yayin da jami’an hukumar tsaron suka kai karar Kasali zuwa ma’aikatan kula hakkin mata da kananan yara, daga nan kuma sai mahaifiyar yaran tazo ta kwashe yayanta.

Zaku iya bibiyan labaran mu a nan, ko a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel