Mutane hudu sun mutu bayan karo tsakanin yan sanda da masu satan mutane

Mutane hudu sun mutu bayan karo tsakanin yan sanda da masu satan mutane

- An kashe mutane hudu a cikin wani karo tsakanin masu satan mutane da jami’an yan sanda a jihar Lagas

- Al’amarin satan ya afku ne a hanyar Ibeju-Lekki dake jihar Lagas

- Budewar bakin bindiga ya yi sanadiyan mutuwan masu satan mutanen

An kashe wasu da ake zargin masu sace mutane ne guda hudu a ranar Juma’a, 16 ga watan Disamba, bayan sun yi karo tare da wasu jami’an yan sanda daga hukumar yan sandan jihar Lagas.

Mutane hudu sun mutu bayan karo tsakanin yan sanda da masu satan mutane
Mutane hudu sun mutu bayan karo tsakanin yan sanda da masu satan mutane
Asali: UGC

Bincike ya bayyana cewa tawagar yan sandan sunyi nasarar ceto wani likita dake aiki a St Francois Hospita, Onikan, wanda aka bayyana sunan sa a matsayin Dr. Ajayi, wanda kungiyar masu satan mutanen suka sace.

Jaridar Punch Metro ta ruwaito cewa an sace Ajayi a ranar Juma’a, 9 ga watan Disamba, 2016, daga yan bindigan wanda suka kai hari asibitin kuma suka tafi da wasu muhimman abubuwa.

KU KARANTA KUMA: Manyan jaruman Kannywood maza 10 a shekarar 2016

An rahoto cewa an sanar da al’amarin gay an sanda, shine kuma aka fara farautan wadanda ake zargin.

Yan kwanaki bayan harin, an bayyana cewa wadanda ake zargin sun bude fagen tattaunawa tare da yan uwan wanda abun ya shafa, inda suka bukaci a biya kudin fansa.

An ce daga baya a ka ga masu satan tare da wanda aka sace a wani kurkumin dake a Ibeju-Lekki dake jihar Lagas.

Jami’in hulda da jama’a na jihar, SP Dolapo Badmos, ya tabbatar da al’amarin, inda ya kara da cewa yan sandan jihar bazasu kuma amincewa da satar mutane ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel