Karanta kaga dimbin tarin arzikin da surukin Buhari, Indimi ya mallaka

Karanta kaga dimbin tarin arzikin da surukin Buhari, Indimi ya mallaka

A duk lokacin da kaji an kira sunan ‘Indimi’, lallai ka sani cewa shine hamshakin dan kasuwan dake da mallakin kamfanin harkar mai da iskar gas mai suna ‘Oriental Energy’.

Karanta kaga dimbin tarin arzikin da surukin Buhari, Indimi ya mallaka
Iyalan Buhari da Surukinsu

Kasancewar yaron Muhammed Indimi, wato Ahmad Muhammad Indimi ya auri yarinyar shugaban kasa, Zahra Buhari, hakan na nuni da cewa attajiri Muhammad Indimi ya zama suruki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kenan.

KU KARANTA:Karin hotuna daga auran Zahra da Ahmed Indimi

Wannan ke nuna cewa iyalan gidan Alh Indimi suna da babban buri a rayuwa, musamman wajen gwama mulki da arziki, wanda shike baiwa kowane mutum karfin iko a rayuwa.

Idan baka sani ba ka sani, har ila yau, Muhammed Indimi suruki ne ga tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida, kuma suruki ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, baya ga cewa abokinsa ne, sa’annan suruki ne ga mai kudin Afirka Aliko Dangote.

Karanta kaga dimbin tarin arzikin da surukin Buhari, Indimi ya mallaka
Muhammad Indimi

Attajiri Muhammadu Indimi shine shugaba kuma wanda ya assasa kamfanin mai da iskar gas Oriental Energy, kuma jaridar Forbes ta kiyasta arzikinsa da suka hada da kadara da kudi sun kai dala miliyan 670 ($670m), kimanin sama naira biliyan dari biyu kenan (N 211050000000).

Tabbas ba zaka raba tsakanin dan Adam da kudi ba, ko dan adam da son mulki ba.

Ku cigaba da bibiyan labaran mu a nan, ko nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel