An wanke ni – Murtala Nyako

An wanke ni – Murtala Nyako

- Tsohon gwamnan jihar adamawa Murtala Nyako ya bayyana ra’ayinsa ga hukuncin kotun koli dangane da hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke

- Tsohon gwamana jihar Adamawa ya ce kotun koli ta wanke shi

- Ya ce zai koma ya ci gaba da noma da kuma bada shawarwari ga mutanen Adamawa da Najeriya baki daya.Tsohon gwamnan yace zai koma yaci gaba da noma

An wanke ni –Murtala Nyako
An wanke ni –Murtala Nyako

Tsohon gwamnan iahar Adamawa Murtala Nyako ya bayyana rayinsa dangane da hukuncin kotun koli dangane da hukuncin da kotun daukaka karar aakan tsigeshi da aka yi .A hirarsa da ‘yan jarida bayan yanke hukuncin a ranar juma’a 16 ga Disamba, Nyako ya ce kotun koli ta wanke shi.

Tsohon gwamnan ya ce, kotu ta wanke shi ga duk wasu zarge zarge da ake yi masa. Ya kuma ce kotu ta tabbatar da cewa tsigeshi da aka yi baya kan doka da oda. Nyako ya kara da cewa, yana godiya ga Allah da ya ba shi dama na bautawa al’ummar jihar Adamawa har na tsawon shekaru takwas na zagon mulki.

Ya ce, “na yi iyaka kokarina a lokacin da na ke gwamnan jama’a wajen kawo abubuwan more rayuwa da kuma wurare kamar ilimi, da lafiya, da harkar noma, da gina tituna, da kuma bunkasa alumma.

“Ina son na yi aikina na bada shawarwari masu ma’ana, da bada gudunmawa ga mutanen Adamawa da kuma Najeriya baki daya. Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da mara masa baya, su kuma kasance masu bin doka da oda domin cigaba. Babbar kotun a ranar juma’a, 16 ga Disamba ta kori karar da Nyako ya shigar a kan ta ya koma kan mukaminsa na gwamnan jihar Adamawa da aka tsige shi a bai kammala wa’adinsa ba. Nyako a karar da ya daukaka ya ce hakan zai bashi dammar karasa shekarunsa guda biyu a matsayin gwamnan jihar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel