Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 24 a jihar Taraba

Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 24 a jihar Taraba

Rahotanni daga jihar Taraba sun nuna cewar kimanin mutane 24 ne suka rasa rayukansu yayin da wata rikicin kabilanci ta barke tsakanin kabilar Tiv da kabilar Fulani a kauyen Sabon Gida dake garin Dan Anacha.

Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 24 a jihar Taraba
Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 24 a jihar Taraba

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar anyi asarar dukiya na dimbin nairori, sa’annan jama’a da dama sun bace.

Majiyar mu ta bayyana mana cewar an rikicin ya fara ne tun a ranar Asabar lokacin da aka tsinci wasu gawawwakin yan Fulani a wani daji, ganin haka ya sanya sauran jama’an kabilar Fulani daukan makami inda suka je kauyen yan Tiv domin daukan fansa.

KU KARANTA:Karfin hali! Tsohuwa da yin fashi

“na kirga gawawwaki 20 da muke tsammanin an kashe su ne da safiyar ranar Lahadi” inji wani mazaunin kauyen. Maiyar ya kara da cewa “mun rasa inda yayanmu kanana da iyaye mata suka shiga tun bayan harin”

Da aka tuntubi Kaakakin rundunar yansandan jihar Taraba, David Misal, ya tabbatar da faruwar rikicin, inda yace rundunar ta aika da karin jami’an tsaro kauyen da abin ya faru don tabbatar da zaman lafiya da bin doka.

Sai dai David Misal yace rundunar yansandan jihar ba zata iya tabbatar da adadin mutanen da aka hallaka ba, har sai ta kammala gudanar da bincike.

Ku cigaba da bibiyan labaran mu a nan, ko a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel