Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)

Aure tsakanin yar shugaban kasa Muhammadu Buhari da Aisha Buhari tare da dan biloniya Muhammadu Indimi, Ahmed ko kusa bai zo dai-dai da yanda shugaban kasa ya so ya kasance ba ta fannin sauki.

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
Zahra Buhari da Ahmed Indimi

Duk da haka, wasu fitattun yan Najeriya sun samu gayyata na wasu daga cikin tsadaddun liyafar da aka shirya na bikin.

1. Darey Art Alade

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
Darey Art Alade

Shine ya shirya kwallon bikin Zahra da Ahmed

2. Ayo Makun aka AY

Mai wasan barkwanci AY
Mai wasan barkwanci AY

Dan wasan barkwancin kamar Darey Art Alade ya samu damar halartan bikin Zahra da Ahmed.

3. Adekunle Gold

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
Adekunle Gold

Mawakin YBNL ya samu halartan bikin inda ya yi wasu daga cikin wakokinsa.

Dangantakar dake tsakanin Zahra Buhari da Adekunle Gold ya wuce na masana’atar nishadantarwa kamar yadda su biyun sun kasance abokan juna tun ma kafin shugaba Buhari ya hau mulki a 2015. Su dukka biyun sun kasance masu goyon bayan masu cutar sikila. Sun kuma kasance jakadun gidauniyar ta Sickle Cell Aid Foundation (SCAF) a Najetriya.

4. Kiss Daniel

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
Kiss Daniel

Shima ya yi wasa a gurin taron

5. Seyi Shay

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
Seyi Shay

Bayan wasa da tayi a gurin bikin Ahmed da Zahra, Seyi Shay ta fito cikin kyakyyawan shiga a gurin taron.

6. Di’Ja

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
Di'ja

Ya kasance abu mai sauki kasancewar Di’ja a cikin jerin mawakan da suka yi wasa a gurin taron kamar yadda ta ksance yar arewa kuma tana da masoya a gurin.

7. DJ Jimmy Jatt

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
DJ Jimmy Jatt

Makidi (DJ) mafi shahara a Najeriya ya kasance wanda aka dauko na musamman don kida a gurin taron.

8. Comedian Senator

Fitattun yan Najeriya da suka halarci bikin Zahra Buhari (hotuna)
Comedian Senator

Ya halarci gurin inda ya nishadantar da jama’a sosai a gurin taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel