Garin dadi na nesa! Hotuna 6 na cikin jirgin shugaban Amurka

Garin dadi na nesa! Hotuna 6 na cikin jirgin shugaban Amurka

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump zai anshi ragamar kasar nan ba da dadewa a farkon shekara mai kamawa. Tare da shigewa fadar shugaban kasar ta Amurka na White House zai kuma anshi babban jirgin jigilar shugaban kasar mai daraja ta daya wanda ake kira da 'Air Force one'.

Shi dai wannan jirgin yana daya daga cikin alamun karfin kasar ta Amurka da kasaitar ta saboda yadda aka kera shi da girma kuma cike da kayan alatu da abubuwan ban sha'awa.

Ga wasu hotuna 6 nan na jirgin da zai barka cikin annashuwa da al'ajabi:

1. Dukkan siffar jirgin

Shidai jirgin an kera shine don ya dauki mutanen da basu da yawa sosai don kuwa mutane dari kawai ya ke iya dauka banda masu tukin sa da sauran ma'aikatan jirgin kamar su injiniyoyi da sauran su. Akwai dakunan bacci da na yin taro da dakin girki duk a ciki.

Garin dadi na nesa! Hotuna 6 na cikin jirgin shugaban Amurka
Garin dadi na nesa! Hotuna 6 na cikin jirgin shugaban Amurka

2. Dakin Bacci

Tabbas babban jirgi ne don kuwa hadda wurin rumtsawa akwai idan an gaji. Akwai wani sashe da aka ware don masu son yin bacci. Tirkashi!

3. Dakin taro:

Akwai dakin taro a cikin jirgin da ake kira John F. Kennedy. Idan akwai abubuwan da za'a tattauna acikin jirgin, akwai dakin taro.

Garin dadi na nesa! Hotuna 6 na cikin jirgin shugaban Amurka
Garin dadi na nesa! Hotuna 6 na cikin jirgin shugaban Amurka

4. Ofisoshi:

Akwai ofisoshi a cikin jirgin. Akwai ofisoshin sojoji da sauran jami'an tsaron da shugaban kasar yake tafiya dasu. Akwai ofisosin yan jarida da dai sauran su.

5. Wurin hutawa:

Wurin hutawa kuma a cikin jirgin shine inda ake hutawa idan angaji. Ko shakka babu shugaban kasar Amurka yana aiki sosai ba dare-ba-rana. To kam dole ne ya gaji kuma ya bukaci hutu.

6. Wurin shakatawa:

Duk baya da watannan kayan alatun da ke akwai a jirgin, akwai kuma wurin shakatawa. Akwai inda mutum zai kalli talabishin ko yayi anfani da yanar gizo-gizo kai harma da wasanni musamman don anfanin kananan yaran da ake tafiya da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel