An kashe diyar tsohon shugaban kasar Mozambique

An kashe diyar tsohon shugaban kasar Mozambique

– Diyar tsohon shugaban kasar Mozambique ta bakunci lahira Ranar Laraba

– ‘Yan bindiga sun harbe Diyar Tsohon Shugaba Armando Guebuza

– An harbe ‘Yar Ta’alikar a Garin Maputo; ana zargin Mijin ta

An kashe Diyar Tsohon Shugaban Kasar Mozambique
An kashe Diyar Tsohon Shugaban Kasar Mozambique

A kasar Mozambique dai Diyar Tsohon Shugaban Kasar aka kashe. ‘Yan Bindinga sun harbe Misis Guebuza wanda hakan yayi sanadiyar ajalin ta. Diyar Shugaban tana da shekaru 36 a Duniya. Wannan abu ya faru ne kwanan biyu da suka wuce a Babban Birnin Maputo.

Diyar Tsohon Shugaban ta sha harbi ratata a jikin ta, kafin a kai Asibiti, ta cika. Jaridar Kasar tace yanzu haka an kama Mijin Diyar Tsohon Shugaban Kasar. ‘Yan Sanda sun yi ram da Zofina Mujane da zargin cewa shi ya kashe matar sa.

KU KARANTA: Shk Buhari ya …

Mijin na ta Mujane yayi aiki da Kamfanin Sigari ta Turawa. Misis Guebuza kuma Babbar Ma’aikaciya ce kuna Hamshakiya a Kamfunan sadarwa, tana kuma cikin harkar kasuwancin gidan na su. Shekaru biyu da suka wuce ne dai tayi aure da Zofina Mujane inda mutane kusan 2000 suka halarta.

Misis Guebuza dai tana cikin manyan mata da ake ji da su a Duniya. Jaridar Forbes ta saka ta cikin manyan matan Duniya. A jerin hamshakan ‘yan mata na nahiyar Afrika, ita ce ta 7.

Asali: Legit.ng

Online view pixel