Zan so in buga kwallo da Messi a kungiya daya - Ronaldo

Zan so in buga kwallo da Messi a kungiya daya - Ronaldo

Gwarzon dan kwallon Duniya, Christiano Ronaldo ya bayyana sha’awarsa na son buga wasa tare da Lionel Messi a kungiya daya don ya samu damar kara lashe kyautan gwarzon dan wasan kwallon Duniya.

Zan so in buga kwallo da Messi a kungiya daya-Ronaldo
Zan so in buga kwallo da Messi a kungiya daya-Ronaldo

Ronaldo wanda ya lashe kyautan gwarzon dan kwallon duniya na bana a satin daya gabata ya bayyana cewa ya kamata a ce gwarazan yan kwallo kamar shi da Messi su buga wasa a kungiya daya.

A bikin bada kyautukan gwarzon kwallon kafa na bana, Lionel Messi shi ke biye da Ronaldo, inda ya zamto na biyu.

Da yan jarida suka tambayi Ronaldo ko yana ganin da ya lashe kyatan dayawa inda yana buga kwallo tare da Messi, sai yace “wannan tambayar nada wuyan amsa, gaskiya ban sani ba.”

KU KARANTA:Dr Osato: Dan Najeriya mai digiri 11

Ya cigaba da cewa “zan so in ganni ina buga wasa tare da shi a kungiya daya. ina ganin ya dace ace manyan yan wasa suna buga kungiya daya, don da zamu buga wasa tare a kungiya daya, toh da na lashe kyautan fiye da shi, shi ne zai dinga bina a baya. kowa ya san Messi babban dan wasa ne, ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar.”

Ronaldo yace yana fatan ya kamo Messi a shekarar 2017 mai zuwa, yace: “zan cigaba da kokari, amma yanzu abinda ke gabana shine mu lashe kofin zakarun kungiyoyin duniya. Bayan wannan, sai muci La Liga, sai kofin zakarun nahiyar turai, da kuma Copa del Rey, ina so na lashe komai”

Ku cigaba da bibiyan labaran mu a nan, ko a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel