Jihar Plateau ta gano ma’aikatan bogi da dama

Jihar Plateau ta gano ma’aikatan bogi da dama

– Gwamnatin jihar Plateau tace ta gano ma’aikata sama da 500 na bogi a Jihar

– Kwamishinan kudi ta jihar, Tamwakat Weli ta bayyana haka

– Duk wata suna lashe kudin Jihar a banza

Jihar Plateau ta gano ma’aikatan bogi da dama
Jihar Plateau ta gano ma’aikatan bogi da dama

A jihar Plateau an gano ma’aikatan karya da ke cikin lalitar gwamnatin jihar. Gwamnatin jihar tace ta gano Ma’aikata kusan 579 na bogi. Kwamishinan Kudi ta Jihar, Tamwakat Weli ta bayyana haka a Ranar Talata.

Tamwakat Weli tace an samu fiye da Ma’aikata 100 da za su mayar da kudin da suka karba. Ana san samu sama da Miliyan 70 a hakan. Kwamishinar tace an gano Ma’aikatan bogin ne bayan wani bincike da aka gudanar.

KU KARANTA: 'Yar Majalisa ta rasu a Landan

Kwamishinar tace Jihar na bukatar kudi Naira Biliyan 4.7 domin biyan Ma’aikata ragowar kudin su. Tace ana jiran wasu kudi da har yanzu ba su gama shigowa ba.

A cikin wannan yanayin ni-‘yasun da tattalin arzikin kasar Najeriya ke ciki ne dai, Gwamnatin Jihar Bauchi tace ta gano ma’aikata na bogi sama da 6, 000 a fadin Jihar kwanaki. Haka Gwamnatin Jihar Kaduna ta Malam Nasiru El-Rufai ta sanar da cewa ta gano ma’aikata fiye da 13,000 na bogi a Jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel