Yar majalisar jihar Delta ta mutu a asibiti

Yar majalisar jihar Delta ta mutu a asibiti

- Majalisar jihar Delta tayi rashin daya daga cikin daddadun mambobinta, Misis Omawumi Udoh

- Misis Omawumi Udo dake wakiltan kudancin Warri ta mutu a wani asibiti dake birnin Landan bayan wani rashin lafiya da ya kama ta

- An bayyana Misis Udoh a matsayin mace tamkar da dubu, wacce ta yi tsawon rauwarta cikin aiki, soyayya, tausayi da jajircewa ga iyalinta, gari da kuma jihar

Yar majalisar jihar Delta ta mutu a asibiti
Yar majalisar jihar Delta ta mutu a asibiti

Majalisar jihar Delta tayi rashin daya daga cikin daddiyar mambanta, Misis Omawumi Udoh.

Cif Monday Igbuya, kakakin majalisar, ya sanar da mutuwar Misi Omawumi Udoh dake wakiltan kudancin Warri a daren ranar Laraba. Ta mutu ne a wani asibitin Landan bayan tayi fama da wani rashin lafiya.

KU KARANTA KUMA: Hotuna daga bikin Zahra Buhari

Kakakin a wata sanarwa dauke da sa hannun Henry Ebireri, sakataren labaransa, Igbuya ya bayyana marigayiya Udoh a matsayin “jarumar mace kuma shugaba.

Kakakin ya kuma bayyana Udoh a matsayin mutun na daban, wacce ta yi rayuwa cikin aiki, soyayya, tausayi da kuma kokari ga iyalanta, garinta da kuma jihar baki daya.

A cewar sa, mutuwar Omawunmi Udo ya kasance babban rashi ga jihar.

Kakakin ya roki Ubangiji da ya ji kan Udoh ya gafarta mata sannan kuma y aba yan uwanta karfin jure wannan rashi da sukayi.

Udoh wacce aka Haifa a 1960. Ta zama yar majalisar jihar a 2003, a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel