Farashin kayan abinci ya karye a jihar Legas

Farashin kayan abinci ya karye a jihar Legas

An samu raguwar farashin kayayyakin abinci sosai a jihar Legas yayin da bikin kirismeti ke karatowa.

Farashin kayan abinci ya karye a jihar Legas
Farashin kayan abinci ya karye a jihar Legas

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewar farashin tumaturi da tarugu ya fadi warwas a kasuwanni da daman a garin jihar Legas da kashi 55. Binciken da muka yi ya bayyana cewar farashin kwandon tumaturi daya kai N9,000 a baya, a yanzu ya sauko naira N5,000 a kasuwannin Mile 12 da Iddo.

Haka zalika farashin Tattasai da Attarugu sun sauko zuwa N4,500, da N4000, ba kamar yadda suke N8,000 ba a a watan Nuwamba. Buhun Albasa da ake siyar da shi kan N28,000 ya dawo N17,000, Shima Garri ba’a barshi a baya ba, a yanzu ana siyar da shi a kan N650. A kasuwan Daleko ma ana siyar da buhun shinkafa tsakanin N16,000 zuwa N24,000.

KU KARANTA:Messi ya faranta ma wani yaro dan kasar Afghanistan rai

Kaakakin yan kasuwan Mile 12 Femi Odusanya ya bayyana dalilin saukowar farashin da samun albarkan kayan noma mai yawa a wannan shekarar.

Yace: “Yawancin manoma na fitar da kayan gonarsu a yanzu, don haka kayan sunyi yawa a kasuwa, dalili kenan daya sanya karyewar farashin. Muna mika kokon barar mu ga gwamnatin tarayya data yi amfani da na’urorin zamani wajen adana sauran amfanin gonar da aka samu, don cin moriyarsu a nan gaba, bamu son sake maimaituwar abinda ya faru a baya sakamakon rashin tattala amfanin gonakin mu.”

Farashin kayan abinci ya karye a jihar Legas
Farashin kayan abinci ya karye a jihar Legas

Daga karshe Odusanya yayi kira ga gwamnati data dauki matakan gaggawa don habbaka cigaban harkar noma. Sai dai wata yar kasuwa mai suna Yinka Okunola ta danganta hauhawan farashin shinkafa da karancin shinkafar gida a kasuwanni.

Tace “bamu da shinkafar gida a kasuwannin mu, amma da ace akwai shi, za’a samu saukin farashin dukkanin shinkafar”

Ku cigaba da bibiyan labaran mu a nan, ko a nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel