Hukuncin Kanu: Maganganu 5 da Nnamdi Kanu yayi akan Buhari a kotu

Hukuncin Kanu: Maganganu 5 da Nnamdi Kanu yayi akan Buhari a kotu

A ranan Talata, 13 ga watan Disamba, shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu da wasu guda 3 sun gurfana a gaban kotu na laifin yaudarar kasa,kirkiro kungiya, tayar da tarzoma.

Hukuncin Kanu : Maganganu 5 da Nnamdi Kanu yayi akan Buhari a kotu
Hukuncin Kanu : Maganganu 5 da Nnamdi Kanu yayi akan Buhari a kotu

A gurfanar, Alkaliyar mai sharia, Justice Binta Nyako,ta yanke cewa za’a yi masa gurfanar asiri kamar yadda hukumar DSS a nema. Tace za’a sakaye sunayensu kuma babu wanda zai gansu.

Amma bayan yanke hukuncin, Kanu ya fara tayar da tarzoma a cikin kotun,yace ba zai yarda a yi masa gurfana a asirce ba.

KU KARANTA: Matashi zai hallaka kansa

Kawai sai ya far wasu maganganu akan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ga jerin kalaman da yayi akan shugaba Buhari:

1. “Yana son gurfanar da ni a asirce? Ana kashe mutane na, bayan haka kace zaka gurfanar da ni a asirce?”

2. “Mahaukaci ne! Ku fada Buhari abinda nace, shi mahaukaci ne! Ba zai iya tsare ni ba, mahaukaci ne.”

3. “Baku bi umurnin kotu,kuma kuna cewa zaku gurfanar da ni a asirce. Kai mahaukaci ne? Shirme,ba zai yiwu ba.”

4. “Lokacin da Buhari ke magana na a cikin jama’a ,me ya faru,me yasa ba kare maganganunsa ba?”

5. “Shi yake nada alkalai, Buhari ya kasance yana nada alkalai a wannan kasa,ya daina barazana ga alkalai,shirme ne! Ba zan yarda ba.”

Ku kasance tare da mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa, https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel