Zaben Rivers: APC ta tafka mugun magudi Inji PDP

Zaben Rivers: APC ta tafka mugun magudi Inji PDP

– PDP tace APC ta bayyana yadda APC tayi amfani da Jami’an tsaro wajen magudi a zaben Rivers

– PDP tace Hukumar INEC ta nuna bambamci

– Jam’iyyar PDP tace da Gwamnatin Tarayya tayi takara ba APC ba

Zeben Rivers: APC ta tafka mugun magudi Inji PDP
Zeben Rivers: APC ta tafka mugun magudi Inji PDP

Jam’iyyar PDP tace an yi amfani da Jami’an Sojoji wajen yin magudi na Inna-na-naha a Zaben Rivers. Bangaren Ahmed Makarfi na PDP suka ce APC ta tafka mugun magudi a zaben da ya gudana cikin kwanakin nan.

Mai magana da bakin Jam’iyyar PDP, Dayo Adeyeye Jam’iyyar su tayi takara ne da Soji, Hukumar zabe da kuma APC. Adeyeye ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar da Birnin Abuja. APC ta samu Sanata daya ne kadai a zaben, sai dai PDP tace sam magudi aka yi har Magnus Abe yaci zaben.

KU KARANTA: Hadarin mota ya kashe mutane a Katsina

Gwamnan Jihar, Nyesom Wike ya sha alwashin cewa ba zai kara ba Jami’an tsaro wani agaji ba a Jihar sa saboda irin magudin da aka tafka da su. Gwamnan dai ya tara Jama’a inda suka tsaya tsayin-daka cewa INEC ba za ta murde masu zabe ba.

Sai dai APC tace ba za a bugi yaro a hana sa kuka ba. PDP dai tace Gwamnatin Tarayya ce ta turo Minista, Rotimi Amaechi domin murde zaben. Sojoji dai sun ce ba su yi wani ba daidai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel