Hakikanin gaskiyar lamarin? Saboda kishi ta yada bidiyon mijinta da matarsa suna sumbantar juna

Hakikanin gaskiyar lamarin? Saboda kishi ta yada bidiyon mijinta da matarsa suna sumbantar juna

Wani bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ake nuna wani mutum dattijo da wata mata suna sumbatar juna ya yi ta jawo cece-kuce a tsakanin jama'a, musamman ma dai a jihar Zamfara, jihar da aka ce mutumin ya taba wakilta a majalisar kasa.

Hakikanin gaskiyar lamarin? Saboda kishi ta yada bidiyon mijinta da matarsa suna sumbantar juna
Hakikanin gaskiyar lamarin? Saboda kishi ta yada bidiyon mijinta da matarsa suna sumbantar juna

Daga bisani bayanan dake fitowa sun wanke wannan bawan Allah, wanda aka ce sunan sa Sanata Sahabi Ya'u Kaura inda aka gano wanda ke bidiyo din Sarkin Bodinga ne da matarsa. Sannan ita ma matar da wasu suka yi wa zargin ba matar sa ta aure ba ce, an bayyana sunanta na ainihi Sa'adatu Galadima kuma matar Sarki ne ne ba Saneta ba.

Sai dai yadda aka yi wannan bidiyo da aka dauke shi a sirrance ya bayyana a zaurukan sada zumunta, wanda kuma ya haifar masa da tofin Allah tsine, shi ne abin da jama'a suka yi ta tambaya.

Wani sautin murya da ya fito daga baya bayan nan shi ya ba da amsar tambayar da ake yi, domin kuwa a ciki an ji sautin wata mata da wani namiji suna magana game da illar da yaduwar wannan bidiyo ya haifar musu, har ma a ciki take zargin wata mai suna Lubabatu da laifin fara fitar da abin.

Ana dai zargin cewa wannan Lubabatu kishiyar Sa'adatu ce, matar dake cikin bidiyon, kuma a wani hoton kwafin hirar su ta chatting, Sa'adatu ta yi zargin kishi ne ya sa Lubabatu yada wannan bidiyon, domin har tana ce mata, 'ai kishi ba hauka ba ne.'

Shi dai an ce Sarkin ya bayyana cewa, zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, kuma abin da ya faru sirri ne tsakaninsa da matarsa.

Don haka ya kamata su nemi gafarar ubangiji kuma a guji saurin zargi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel