Obasanjo ya roki yan Najeriya a madadin Yan sanda

Obasanjo ya roki yan Najeriya a madadin Yan sanda

- Cif Olusegun Obasanjo ya koka kan hauhawan laifuka a Najeriya

- Tsohon shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su taimaka wa yan sanda gurin rage lafukan da ake fama dasu

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, yayi kira gay an Najeriya musamman masu fada a ji da su ba yan sandan Najeriya goyon baya gurin magance dukkan laifuka.

Obasanjo ya roki yan Najeriya a madadin Yan sanda
Obasanjo ya roki yan Najeriya a madadin Yan sanda

A ranar Litinin, 12 ga watan Disamba, Obasanjo yace yan sanda na fuskantar aiki mai wahala.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro a jihar Ogun, da kuma kaddamar da kamfen din Police Complaint Rapid Response Unit da kuma Change Begins with me a Abeokuta.

A cewar Obasanjo idan ana son yan sandan Najeriya su shiryu kuma su yi nasara a kamfen din ‘Change Begins With Me’ , dole ne sai jama’a gaba daya sun hada hannu da yan sanda gurin tabbatar da cewa sun basu bayanai a kai- a kai don magance laifuka, da kuma kai rahoton masu laifuka ta hanyar lambobin waya.

Obasanjo wanda ya bayyana EPF a matsayin manufa mai kyau daga sufeto-Janar na yan sanda mai ci a yanzu, Ibrahim Idris, yace aikin dan sanda ya kasance hakkin kowa a kasar.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Kaduna: Fani Kayode ya kai hari ga El-Rufai

Yace: “Wannan manufofin ya kasance mai kyau sosai. Aikin tsaron garinmu, karamar hukuma, jiha da kuma kasar ba wai aikin dan sanda kawai bane, aikinmu ne gabaki daya.

“Muyi kokari gurin taimaka wa yan sanda gurin tsaron garuruwanmu. Yan sanda na aiki mai wahala.

“Idan kuna so kuyi aure kuma kuna bukatar tsaro, yan sanda kuke kira, idan aka yi maku fashi a gida, yan sanda kuke kira, idan kayi fada da matarka, yan sanda kake kira.”

Da yake Magana, kwamishinan yan sanda na jiha, Ahmed Iliyasu, yace EPT ya hada da manyan masu ruwa da tsaki kamar irin shugabbanin gari, shugabannin addini, sarakunan gargajiya, dattawan jihohi, manyan jami’an tsaro masu ritaya, da kuma yan siyasa.

KU KARANTA KUMA: Rikicin addini: An kashe kiristoci 800 – shugabannin katolika

Kwamishinan nay an sanda yace zasu taimaka way an sanda gurin samo mafita ga matsalolin tsaro ta hanyar shiga tsakani da kuma kula da garuruwansu. Iliyasu, wanda yace baza’a samu ci gaba mai ma’ana idan babu tsaro, ya bayyana cewa manufofin zai fitar da laifuka a kasar.

Ku karanta wasu labaran namu a nan: https://twitter.com/naijcomhausa da kuma https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Asali: Legit.ng

Online view pixel