Rikicin Kaduna: Fani Kayode ya kai hari ga El-Rufai

Rikicin Kaduna: Fani Kayode ya kai hari ga El-Rufai

-Cif Fani – Kayode ya yi Magana game da rikicin jihar Kaduna

-Tsohon ministan ya bukaci gwamna El-Rufai da ya magance al’amarin yadda ya dace

-FFK yace dole ne El-Rufai ya dakatar da amfani da barazana

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode (FFK) ya kalubalanci Gwamna Nasir El-Rufai, kan yanayin harka a jihar Kaduna.

Rikicin Kaduna: Fani Kayode ya kai hari ga El-Rufai
Rikicin Kaduna: Fani Kayode ya kai hari ga El-Rufai

FFK ya bukaci gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da ya yi koyi da tattaunawa gurin sauraron mutanen kudancin Kaduna maimakon yin barazana da kuma bin bangaren masu laifi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Fani-Kayode yayi wa’azin ne a wata wasika mai taken: “Nasir El Rufai and the blood fest in Southern Kaduna part2” wato Nasir El Rufai da zubar jinni a kudancin Kaduna kashi na 2, a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba.

Ya kara da cewa mutanen na fuskantar wahala kuma sun cancanci kulawa sosai daga gwamnan da kuma gwamnatin.

KU KARANTA KUMA: Rikicin addini: An kashe kiristoci 800 – shugabannin katolika

Fani-Kayode wanda ya bayyana Mallam Nasir El- Rufai a matsayin wani aboki, yace, “Ina jin irin kunci da radadin dake karkashin kalaman sanata La’ah kuma nayi ittifakin biyayyar sa. Mutanen kudancin Kaduna na fuskantar wahala kuma sun cancanci fiye da haka.

“Gaskiyar Magana ita ce kaso 50 cikin 100 na mutanen jihar Kaduna kiristoci ne amma wannan ba shine kudirin gwamna ba don magance hakan.

“Bari mu sa ran cewa abokina kuma dan uwana Gwamna Nasir El Rufai zai saurara kuma ya canja tsarin sa maimakon amfani da barazana ya bi sahun wadanda sukayi kokarin fada masa gaskiya mai daci.

“Mu tuna cewa abokan gaskiya na fadan gaskiya a ko da yaushe, duk kuwa da irin yadda gaskiyar take ga wadanda suke so da kauna."

Asali: Legit.ng

Online view pixel