HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki

HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki

Wani bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ake nuna wani mutum dattijo da wata mata suna sumbatar juna ya yi ta jawo cece-kuce a tsakanin jama'a, musamman ma dai a jihar Zamfara, jihar da aka ce mutumin ya taba wakilta a majalisar kasa.

Dan Sarki ya rubuta kan shafin Facebook na Arewa DailyPost cewa wanda daga bisani bayanan dake fitowa sun wanke wannan bawan Allah, wanda aka ce sunan sa Sanata Sahabi Ya'u Kaura. Sannan ita ma matar da wasu suka yi wa zargin ba matar sa ta aure ba ce, an bayyana sunanta na ainihi Sa'adatu Galadima kuma matar sa ce ta aure.

KU KARANTA: Mu ba barayi bane - Sanatoci sun yi kaca-kaca da Buhari

Sai dai yadda aka yi wannan bidiyo da aka dauke shi a sirrance ya bayyana a zaurukan sada zumunta, wanda kuma ya haifar masa da tofin Allah tsine, shi ne abin da jama'a suka yi ta tambaya.

Wani sautin murya da ya fito daga baya bayan nan shi ya ba da amsar tambayar da ake yi, domin kuwa a ciki an ji sautin wata mata da wani namiji suna magana game da illar da yaduwar wannan bidiyo ya haifar musu, har ma a ciki take zargin wata mai suna Lubabatu da laifin fara fitar da abin.

Ana dai zargin cewa wannan Lubabatu kishiyar Sa'adatu ce, matar dake cikin bidiyon, kuma a wani hoton kwafin hirar su ta chatting, Sa'adatu ta yi zargin kishi ne ya sa Lubabatu yada wannan bidiyon, domin har tana ce mata, 'ai kishi ba hauka ba ne.'

Shi dai tsohon Sanata Sahabi Kaura ya bayyana cewa, zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, kuma abin da ya faru sirri ne tsakanin sa da matarsa.

Don haka ya kamata su nemi gafarar ubangiji kuma a guji saurin zargi. Wannan tana fitowa daga @Zuma Times Hausa

Ku duba wasu hotunan wani Sanata da matarsa a kasa:

HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki
HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki

HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki
HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki

HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki
HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki

HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki
HOTUNA: Saboda kishi ta yada bidiyon wani tsohon Sanata da matarsa - Habu Dan Sarki

Asali: Legit.ng

Online view pixel