Ku dan kara hakuri dai, Inji Shugaba Buhari

Ku dan kara hakuri dai, Inji Shugaba Buhari

– A sakon Bikin Mauludi na bana, Shugaban Kasan yace Jama’a su kara hakuri da Gwamnatin sa

– Shugaba Buhari yace ka da a karaya, Najeriya za tayi kyau

– A jiya Litinin aka yi Hutun Maulud a Najeriya

Ku dan kara hakuri dai, Inji Shugaba Buhari
Ku dan kara hakuri dai, Inji Shugaba Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu ya kira ‘Yan Najeriya da su kara hakuri da Gwamnatin sa. Shugaban Kasar yace ka da ‘Yan Najeriya su karaya, tabbas Najeriya za tayi kyau nan da wasu ‘yan lokaci.

Shugaban Kasan yace ka da a gaji a sakon Bikin Mauludi ga ‘Yan Kasar. Ranar Mauludin ta kama Lahadin nan ne da ta wuce. Hakan ta sa aka bada hutu a jiya, Litinin. Shugaba Buhari yace ba za a dawwama a cikin wannan yanayi da ake ciki ba yanzu.

KU KARANTA: Shinkafar gida tayi kasuwa da Kirismteti

A Rana irin ta Mauludi ne wasu Musulmai a Duniya ke yin Bukukuwa da dama wajen nuna murnar haihuwar Annabi Muhammadu SAW. Shugaba Buhari yace zuwa shekara mai zuwa, Najeriya za ta tsallake wannan rikici na Tattalin Arziki.

A wata damawar kuma, Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Femi Adesina yace maganar cewa Shugaba Buhari ya sauke Hafsun Sojin Kasar ba gaskiya bane.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel