APC ta rushe dakatar da Shehu Sani

APC ta rushe dakatar da Shehu Sani

– Jam’iyyar APC ta warware dakatarwar da aka yi wa Sanata Shehu Sani

– APC ta Jiha ta dakatar da Sanatan, Sai dai an ce dakatarwan ya saba doka

– Shehu Sani yace ba uban da ya isa ya dakatar da shi daga Jam’iyya

APC ta rushe dakatar da Shehu Sani
APC ta rushe dakatar da Shehu Sani

APC na Arewa-maso-Yamma ta rushe dakatarwar da aka yi wa Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya. Jam’iyyar tace matakin da bangare na Jihar suka dauka na dakatar da Sanatan Shehu Sani bai bi ka’ida ba.

Jam’iyyar tace kafin a tsaida da ko kore sa daga Jam’iyya sai an cika wasu sharudda, wanda APC na Jihar ba ta bi ba. Ana ta takaddama dai tsakanin Sanatan mai wakiltar Kaduna na tsakiya da kuma Gwamnan Jihar Malam Nasiru El-Rufai.

KU KARANTA: Rudani a Gidan Soji

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Bangaren Arewan, Inuwa Abdulkadir yace matakin da Bangaren Jam’iyyar na Jihar suka dauka ya saba dokar Jam’iyya, kuma hakan na iya haifar da rikici. Inuwa Abdulkadir yace a cikin gida za a magance wannan matsalar.

Sanata Shehu Sani dai yace babu wanda zai iya korar sa daga Jam’iyya, duk da ya saba yin fito-na-fito da Gwamnan Jihar. Malam Nasiru El-Rufa’i dai yace dokar Kasa ta ba kowa wage baki yarda ya ga dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel