Gobara tayi mummunar ta'asa a Sokoto

Gobara tayi mummunar ta'asa a Sokoto

Kimanin mutane 12 ne suka mutu a sakamakon gobara har 385 da aka samu a jihar Sokoto tun daga watan Janairu kawowa yanzu a shekarar nan inji shugaban hukumar kula da gobara Alhaji Ibrahim Dingyadi.

Gobara tayi mummunar ta'asa a Sokoto
Gobara tayi mummunar ta'asa a Sokoto

Alhaji Ibrahim ya bayyana hakan ne a taron da yayi da manema labarai a jihar inda ya ci gaba da cewa an tafka hasarar da takai N2.1biliyan a shekarar.

Shugaban ya kuma kara da cewa hukumar tasa ta kuma yi nasarar tseratar da dukiyar da ta kai darajar N2.8 biliyan.

Dingyadi ya kara da bayyana cewa dayawa daga gobarorin da aka samu a jihar sun samu asali ne daga wutar lantarki.

Sannan sai ya cigaba da cewa: “Maikata ta ta dukufa wajen ganin an wayar ma da jama'a kai kan illolin gobara da kuma yadda za'a kare kai daga gareta.

“Muna kuma kara wayar ma da jam'a kai game da kai rahoton barkewar gobara ga hukuma cikin gaggawa.”

Sannan kuma sai yayi albishir din cewar a kwanan baya ma gwamnatin ta jihar ta bayar da kwangilar siyo motocin kashe gobara har 10 sannan kuma yace biyar daga cikin wadan da ke akwai yanzu haka ana yi masu garambawul.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel